Connect with us

News

Kotu ta tura tsohon Ministan Makamashi kurkuku, bayan tartsatsin harƙallar wutar Mambilla 

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Kotu ta tura tsohon Ministan Makamashi kurkuku, bayan tartsatsin harƙallar wutar Mambilla ya babbake rigar sa

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon Ministan Makamashi da Ƙarafa, Olu Agunloye, bisa tuhumar sa da aikata laifuka bakwai a harƙallar kwangilar dala biliyan 6 ta tashar wutar lantarki ta Mambilla, aikin da ko tubalin toka ba a gina.

Advertisement

Agunloye dai ana zargin sa da bada kwangila ta wuru-wuru a Babbar Kotun Abuja da ke Apo, Abuja.

Betta Edu: ACM ta shirya gudanar da zanga-zanga a Kaduna, Abuja muddin Tinubu bai dakatar da Ministan Cikin Gida, Tunji-Ojo ba

Ya shaida wa Mai Shari’a cewa bai aikata laifin da ake tuhumar sa ba.

Advertisement

Ya yi musun zargin da ake yi masa a lokacin da Mai Shari’a J.O Onwuegburzie ya karanto masa tuhumar da ake yi masa, a ranar Laraba.

Daga nan sai Mai Shari’a ya ce a je a kulle shi a kurkuku, kafin ranar da za a saurari batun beli, ranar Alhamis.

Advertisement

A cikin ɗaya daga tuhume-tuhumen da ake yi masa, an zarge shi da bada kwangilar wuru-wuru ta aikin gina Tashar Wutar Lantarki ta Mambilla mai ƙarfin migawat 3,960.

An zarge shi da bada kwangilar ba tare da amincewar gwamnatin tarayya ba, kuma kwangilar ba ta cikin kasafin kuɗi.

Advertisement

Premium Times ta ruwaito cewa EFCC ta shaida wa kotu cewa bada kwangilar ya saɓa wa Doka Sashe na 22(4) ta Haram cin Aikata Zamba, ta 2000.

An kuma zarge shi da karɓar Naira miliyan 3.6 daga kamfanin Sunrise Power cikin Agusta, 2019, shekaru bayan ya bar ofis, ladar-gaben sa na sa gwamnatin tarayya ta amince da kwangilar ga kamfanin.

Advertisement

Wannan laifin ma EFCC ta ce ya saɓa wa Sashe na 8(1)(a) na Dokar Haramcin Aikata Zamba, ta shekarar 2000.

Lauya mai gabatar da ƙara Abba Muhammed, ya roƙi kotu ta sa ranar fara sharia, kuma ta kulle Agunloye kurkuku.

Advertisement

Sai dai lauyan wanda ake tuhumar, wato Adeola Adedipe (SAN), ya shaida wa kotun cewa ai ya cika fam na neman beli.

Mai Shari’a ya tura Agunloye kurkuku, kafin a ji batun ko za a iya bada shi beli a ranar Alhamis.

Advertisement

Wannan gurungunɗuma ta dabaibaye tsohon ministan, har a cikin watan Disamba EFCC ta ce za ta gurfanar da shi, bayan ya kai kan sa ofishin hukumar sakamakon farautar sa da hukumar ta yi.

Tsohon Ministan Wutar Lantarki, wanda EFCC ta buga cigiya da farautar sa a makon da ya gabata, zai gurfana gaban kotu, bayan shafe kwanaki biyar a tsare a hannun jami’an hukumar.

Advertisement

Olu Agunloye zai fuskanci shari’a bayan shafe kwanaki biyar a hannun EFCC.

Ya miƙa kan sa da kan sa a hannun jami’an EFCC a ranar 13 ga Disamba, kwana ɗaya bayan an buga cigiya da farautar neman sa ruwa a jallo, a duk inda ya ke.

Advertisement

Ana zargin sa dangane da karkatar da kuɗaɗe a wata kwangilar biliyoyin dalolin aikin wutar Mambilla, kwangilar da ba a yi aikin ba.

An bayyana cigiya da neman sa ne bayan an ba shi belin kan sa, amma daga baya ya ƙi kai kan sa ofishin hukumar.

Advertisement

Agunloye ya yi Ministan Makamashi a zamanin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo.

Cikin makon jiya ne dai EFCC ta bayyana cigiya da farautar tsohon ministan kan yi wa dala biliyan 6 ‘yar-burum-burum a kwangilar aikin samar da wutar lantarki a Mambilla, aikin da kwata-kwata ba a yi ba.

Advertisement

Kafin ya kai kan sa da kan sa, Hukumar EFCC ta bayyana cigiyar tare da farautar tsohon Ministan Makamashi da Ƙarafa, Olu Agunloye.

EFCC na cigiyar Agunloye ne bisa zargin harƙalla da kuma buga takardun bayanai na fojare a kwangilar aikin wutar lantarki ta Mambilla.

Advertisement

An zargi tsohon ministan da yin daƙa-daƙar bayar da kwangilar aikin wutar lantarki ta dala biliyan 6, a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo, ba tare da tuntuɓar Gwamnatin Tarayya ba.

EFCC ta bayyana cigiya da farautar tsohon ministan a cikin shafin ta na Instagram da kuma Facebook.

Advertisement

A cikin sanarwar, an buga hoton sa, tare da bayyana shekarun sa 75.

Hukumar EFCC ta roƙi duk wani wanda ya gan shi ko ya san inda ya ke, to ya tuntuɓi ko da ɗaya ne a cikin ofisoshin hukumar da ke Benin, Kaduna, Ibadan, Sokoto, Maiduguri, Makurɗi, Ilorin, Enugu, Kano, Legas, Gombe, Uyo, Fatakwal ko na Abuja.

Advertisement

Kakakin EFCC Oladele Oyewale bai yi cikakken bayani dangane da irin nauyin zarge-zargen da ake yi wa Agunloye ba.

Gurumgunɗumar Rikicin Kwangilar Wutar Mambilla:

Advertisement

 

Cikin watan Satumba Agunloye ya fito ya ce a baya EFCC ta bincike shi, har ma ta tsare shi, dangane da batun kwangilar.

Advertisement

 

Ya yi wannan furuci ne bayan tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo ya yi hira da jaridar The Cable, inda ya ce tsohon Ministan Makamashi da Ƙarafa a lokacin da, Olu Agunloye ya bayar da kwangilar aikin wutar Mambilla, ba tare da amincewar Majalisar Zartaswa ta Ƙasa ba.

Advertisement

 

Da farko an bayar da kwangilar wutar lantarkin Mambilla, ga wani kamfani wai shi Sunrise Power and Transmission Limited a cikin 2023.

Advertisement

 

Obasanjo ya yi ƙoƙarin nesanta kan sa daga harƙallar kwangilar, inda ya ce shi bai ma san lokacin da Agunloye ya bayar da kwangilar ba.

Advertisement

 

Raddin Agunloye Kan Obasanjo:

Advertisement

 

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa tsohon Minista ya zargi Obasanjo da nunke ‘yan Najeriya baibai.

Advertisement

 

Tsohon Ministan Makamashi da Ƙarafa, Olu Agunloye, ya zargi tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo da ƙarya da kuma baddala gaskiyar magana dangane da kwangilar aikin wutar lantarki a Mambilla, ta biliyoyin daloli.

Advertisement

 

Da farko dai an bayar da kwangilar aikin a cikin 2003, ga wani kamfani mai suna Sunrise Power and Transmission Limited. Gwamnatin Obasanjo ce ta bayar da aikin gina tashar samar da wutar lantarkin a wancan lokacin.

Advertisement

 

A yanzu batun kwangilar ya daɗe ana shari’a tsakanin kamfanin a kotu a wajen ƙasar nan shi da Gwamnatin Tarayya.

Advertisement

 

A wata tattaunawa da jaridar The Cable kwanan nan, Obasanjo ya ce Agunloye ne ya shirya harƙallar bayar da kwangilar ba tare da amincewar Majalisar Zartaswa ba a lokacin.

Advertisement

 

To amma a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Agunloye ya ƙaryata abin da Obasanjo ya bayyana wa duniya dangane da batun kwangilar.

Advertisement

 

Ya ce ana ƙoƙarin shafa masa baƙin fenti ne, saboda gwamnati na ta borin-kunyar ƙin cika alƙawarin da ta yi a yarjejeniyar kwangilar wutar Mambilla.

Advertisement

 

Ya ce lallai tabbas gwamnatin Obasanjo ta bayar da kwangilar a cikin 2003, inda kamfanin Sunrise and transmission Limited zai samar da babbar tashar wutar lantarki da babu mai girman ta a ƙasar nan, har migawat 3,050.

Advertisement

 

To kuma Agunloye ya ce bayan ya sauka daga muƙamin minista a cikin 2003, sai Obasanjo ya canja shawara, ya ce gwamnatin Najeriya ta ce ita za ta riƙa zuba kuɗi ana aikin, maimakon yarjejeniyar farko, wadda ba Gwamnantin Najeriya ce mai zuba kuɗin aiki ba.

Advertisement

 

Ya ce amma gwamnatin marigayi Umaru ‘Yar’Adua ta soke kwangilar a cikin 2008.

Advertisement

 

Agunloye ya ce Yar’Adua ya soke kwangilar saboda gwamnatin sa ta gano cewa akwai harƙalla a jami’an gwamnatin Obasanjo, tsakanin 2003 zuwa 2007.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending