News
Har yau masu biyan kuɗin wutar lantarki a Najeriya ba su kai mutum miliyan 12 ba – Ƙididdigar NBS
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa, NBS ta bayyana cewa yawan masu biyan kuɗin wutar lantarki ya ƙaru da mutum 240,000 a tsakiyar 2023, inda adadin yawan ya tashi daga miliyan 11.47 zuwa miliyan 11.71.
Wannan ƙididdiga dai ta na nufin har yanzu masu biyan kuɗin wutar lantarki ba su kai mutum miliyan 12 har zuwa ƙarshen 2023 ba.
A ranar Alhamis NBS ta fitar da wannan ƙididdiga a Abuja, mai nuna cewa daga watannin tsakiyar 2023 zuwa watannin kusa da na ƙarshen 2023 an samu ƙarin masu biyan kuɗin wutar lantarki da kaso 2.08 bisa 100.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an yi wannan ƙididdigar bisa ma’aunin yawan bila-bilan biyan kuɗin wutar lantarki, yawan kuɗaɗen shigar da aka samu a watannin da kuma ƙididdigar yawan kwastomomin kamfanonin sayar da wutar lantarki, wato Discos.
Rahoton ya ce an samu ƙarin yawan masu biyan kuɗin wutar lantarki idan aka kwatanta da yawan su a Disamba ɗin 2022, inda a lokacin mutum miliyan 10.94 ne.
Hakan na nuni da cewa an samu ƙarin yawan mutum har kashi 7.09 bisa 100 kenan, daga Disamba 2022 zuwa Disamba 2023.
Wani bincike da aka gudanar kuma cikin watan Yuni, 2023, ya tabbatar da cewa kusan kashi 47 bisa 100 na masu amfani da wutar lantarki a Najeriya, ba su amfani da mita.
