Connect with us

News

Kwalejin Koyar Da Aikin Shari’a Ta Kano Wato Legal Za ta fara karatun Digiri a kwasa-kwasai takwas (8).

Published

on

Kwalejin koyar da aikin shari'a ta Kano wato (Aminu Kano college of Islamic and Legal studies),

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Kwalejin koyar da aikin shari’a ta Kano wato (Aminu Kano college of Islamic and Legal studies), ta sanar da fara karatun Digiri a wasu kwasa-kwasai Takwas.

Shugaban Kwalejin Farfesa Balarabe Abubaker Jakada ne ya sanar da hakan, ta cikin wata sanarwa da Kakakin makarantar Dakta Salisu Ado Marafa ya sanya wa hannu.

Advertisement

Birnin Gwari Ta Fi Kowane Yanki Yawan Albarkatun Ma’adanai A Nijeriya 

Sanarwar ta ƙara da cewa, a ƙoƙarin shugaban makarantar ne a ciyar da Kwalejin gaba, Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Dutsin-ma a Jihar Katsina, ta sahalewar Kwalejin fara bada shaidar Digiri a kwasa-kwasai Takwas.

kwasa-kwasan da Kwalejin za ta bada shaidar Digirin a kansu sun haɗar da, ilimin Turanci (English), Ilimin Arabiyya (Arabic), Ilimin Addinin musulunchi (Islamic Studies), Ilimin Yaren Hausa, Fannin bada shawara da Jagoranci (Guidance and counselling), Ilimin dabarun yin shugabanci (Educational Planning and Administration), Ilimin Na’ura me Kwakwalwa (computer), da kuma fannin tsumi da tanadi (economics).

Advertisement

 

Sanarwar tace za’a fara karatun ne a zangon karatu na gaba, wanda zai fara a watan 6 na wannan shekara ta 2024.

Advertisement

Haka kuma Shugaban Makarantar yace kwalejin za ta ci-gaba da bada shaidar ƙaramar diploma da kamar yadda bayarwa a kwasa-kwasan da ta saba bayarwa.

A ƙarshe Kwalejin tayi fatan masu sha’awar samun shaidar Digiri a waɗannan fannoni, zasu garzaya Makarantar da zarar an fara ɗaukar dalibai, domin ya zama sun shiga sahun farko na ɗaliban da zasu fara cin gajiyar ci-gaban da Kwalejin ta samu.

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending