Interview
VALENTINE’S DAY: Mu Ko Wacce Rana Ranar Soyayyace — Yasir Sani
A Matsayin mu na Mutanen Ƙauye, kowacce rana ranar soyayya ce a gare mu. Duk da haka, keɓance wata rana a shekara da sunan “Ranar Masoya” abu ne da ba ya cikin al’adunmu na Hausa/Fulani, kuma ba mu taɓa jin labarinsa a wajen malaman Musulunci ba.
A duk ranar 14 ga Fabrairu, ana bikin ranar soyayya (Valentine’s Day), inda samari da ‘yan mata ke nuna soyayyarsu ta hanyar aika saƙonni, ba da kyaututtuka, musamman furanni, da sanya kaya masu launin ja da fari, waɗanda ke ɗauke da hoton zuciya.
A wannan rana, wasu ‘yan mata na ziyartar ɗakunan samari, kuma masoya na yi wa junansu duk wani abu da zai basu farin ciki. Abin takaici, a irin wannan rana, adadin matan da ke rasa budurcinsu yana da yawa, sai dai Allah ne kaɗai yasan yawansu.
Abin mamaki, wasu matasan Musulmi sun aro wannan biki suna aiwatar da shi, ko dai don suna ganin sun waye?!
YASIR SANI ABDULLAHI
DAGA JARIDAR INDA RANKA
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
