Connect with us

Interview

Kashi 15 ne kawai ake tuhumarsu yayin da Kano ke samun rahotannin fyade sama da 1,000 duk shekara – NAWOJ

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Kungiyar mata ‘yan jarida ta NAWOJ reshen jihar Kano ta ce daga cikin sama da mutum 1,000 da ake    cin zarafin a duk shekara a jihar Kano kashi 15 ne kawai ake tuhumasu.

Shugabar kungiyar Hafsa Sani Usman ce ta bayyana haka a taron wayar da kan jama’a na yini daya akan ‘yancin dan adam  da jaridar Stallion Times tare da tallafin gidauniyar MacArthur ta shirya a Kano ranar Laraba.

Advertisement

Babu barkewar cutar kyanda a Jihar Kano —Ma’aikatar Lafiya

A cewarta, kararraki sama da dubu daya (1,000) a duk shekara ake shagarwa amma kashi 15 ne kawai ake gurfanar da su a gaban kuliya yayin da kashi 5 kacal ke kai rahoton ga ma’aikatar shari’a domin daukar matakan da suka dace kamar yanda rohotan cibiyar da ke lura da wadanda aka yi wa fyade da sauran nau’ukan cin zarafin mata mai suna WARAKA

Daga nan sai ta bukaci iyaye da masu kulawa da su kara taka tsantsan tare da kai rahoton duk wani lamari na take na  hakkin dan Adam, hakkin yara, da cin zarafi ga hukumomin da abin ya shafa domin dakile wannan annoba.

Shugabar ta bayyana kudurin NAWOJ na hada kai da masu ruwa da tsaki wajen dakile cin zarafin mata da kuma kare hakkin mata.

Advertisement

Shi ma da yake nasa jawabin, babban jami’in kamfanin na Stallion Times, Alhaji Isiyaku Ahmed ya shawarci kafafen yada labarai da su bayar da shawarwarin kare hakkin bil’adama da zamantakewa ta hanyar yada labarai.

Ya ce kafafen yada labarai na da muhimmiyar rawar da za su taka ta hanyar bayar da rahotannin hakkin dan adam da hada kai da kuma bin diddigin shari’o’i don tabbatar da adalci

Ya yi nuni da cewa, makasudin bayar da horon su ne inganta ‘yancin dan adam da hada kai da kuma jin dadin yanayin daidaiton jinsi a cikin al’umma da ci gaba.

Advertisement

A jawabinta mai taken “Understanding Human Rights and Social Inclusion in the Media”, Malama a Sashen Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Bayero Kano (BUK), Farfesa Aisha Isma’il ta bayyana ‘yancin mata a matsayin ‘yancin dan Adam.

Ta bayyana cewa kafofin watsa labaru na iya yin tasiri sosai kan yadda ake fahimtar daidaiton jinsi da haɗin gwiwar zamantakewa, tattaunawa da magance su.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *