Connect with us

News

Cutar Sanƙarau Ta Hallaka Yara 33 A  Sakkwato 

Published

on

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta tabbatar da mutuwar mutane 33 sakamakon ɓarkewar cutar sanƙarau a wasu sassan jihar, yayin da ake ci gaba da samun sabbin masu ɗauke da ita.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Faruk Abubakar, ya ce an samu mutum 256 da ake zargin sun kamu da cutar a ƙananan hukumomi takwas cikin wata guda da cutar ta sake ɓulla.

Advertisement

Kano: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum, Sun Yi Awon-Gaba Da Shanu Sama Da 400 A Gwarzo

A cewarsa, ƙaramar hukumar Sabon Birni ce ke kan gaba da mutum 63, sai Wamakko 60, sannan Shagari 51, Tambuwal kuma 33 da kuma Dange Shuni mai 26.

Advertisement

Ya bayyana cewa mafi yawan mace-macen sun faru ne a cikin al’umma kafin a fara kai marasa lafiya asibiti, sakamakon jinkirin neman magani da kuma ɗaukar cutar a matsayin ƙaramar matsala.

Domin dakile yaɗuwar cutar, gwamnati tare da haɗin gwiwar ƙungiyar kare lafiya ta Duniya Médecins Sans Frontières ta buɗe cibiyoyin killace masu cutar a Dogon Daji da Tambuwal.

Advertisement

Kana Jami’an lafiya sun ce ana ci gaba da karɓar sababbin marasa lafiya, duk da cewa waɗanda aka kai asibiti da wuri na samun sauƙi.

Masana lafiya sun danganta ɓarkewar cutar da cunkoso, zafi da kuma rashin zuwa asibiti da wuri, tare da buƙatar jama’a su rungumi allurar rigakafi da kuma tsaftace muhalli.

Advertisement

 

 

Advertisement

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending