News
Kano: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum, Sun Yi Awon-Gaba Da Shanu Sama Da 400 A Gwarzo
Al’ummar yankin Mainika da ke karamar hukumar Gwarzo sun fada cikin jimami bayan wani mummunan hari da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai wasu kauyukan yankin, inda suka kashe mutane tare da sace shanu sama da 400.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai harin ne a kauyukan Gatari, Sara da Dankendi cikin dare, inda suka rika harbe-harbe domin razanar da mazauna yankin kafin su kwashe dimbin dabbobi.
Hadakar Malamai Sun Bukaci A Gudanar Da Siyasar Kano Cikin Lumana
Wata majiya daga yankin ta shaidawa premier Radio cewa harin ya haddasa firgici da tashin hankali, yayin da mazauna kauyukan suka tsere domin neman tsira.
Da safiyar Alhamis aka gudanar da jana’izar marigayi Abdurrazzak mai shekaru kusan 50, wanda ya rasa ransa a yayin harin.
Marigayin ya bar mata biyu masu juna biyu da kuma yara tara, lamarin da ya kara jefa iyalansa da al’ummar yankin cikin alhini.
Al’ummar yankin sun bukaci hukumomin tsaro da gwamnatin jihar da su dauki matakan gaggawa domin dakile hare-haren ‘yan bindiga da ke ci gaba da barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a a yankunan karkarar jihar Kano.
-
News4 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News2 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News4 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
