News
Dr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
Dr. Muhammed Musa Zango, wanda aka fi sani da Fatah, ya ayyana kudirinsa na tsayawa takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a karkashin jam’iyyar APC, gabanin babban zaben 2027.
Da yake jawabi a wajen taron kaddamarwar da aka gudanar a Kano, Fatah ya ce ya yanke shawarar shiga takarar ne bisa dogon nazari da kuma gogewarsa wajen hulda da al’umma tun daga matakin kasa.
Kwankwaso Ya Ce Bai Yanke Shawara Kan Makomar Siyasarsa Ba Har Yanzu
Ya bayyana cewa tun a shekarar 2003 ya fara tallafa wa kananan ‘yan kasuwa a yankinsa da jari, domin inganta harkokin kasuwanci da dogaro da kai, abin da ya ce ya kara masa kwarin gwiwar shiga siyasa domin wakiltar jama’a yadda ya kamata.
A cewarsa, wakilci nagari shi ne wanda ke sauraron bukatun talakawa tare da mayar da su cikin dokoki da tsare-tsaren da za su inganta rayuwarsu.
Fatah ya kuma gabatar da wasu muhimman manufofi guda bakwai da ya ce za su zama tubalin aikinsa idan aka zabe shi:
Ya ce zai tabbatar da wakilci mai inganci a Majalisar Dokoki ta Kasa, ta hanyar gabatar da kudurori da za su amfanar da jihar Kano.
Haka kuma, ya ce zai mai da hankali kan bunkasa noma domin kara samar da abinci da habaka tattalin arziki.
A bangaren matasa da mata kuwa, ya yi alkawarin samar da shirye-shiryen horaswa da tallafin sana’o’i, tare da kula da masu bukata ta musamman.
Game da kiwon lafiya, Fatah ya ce zai yi kokarin ganin an inganta asibitoci da kuma saukaka samun kulawar lafiya ga al’umma.
Sannan ya jaddada muhimmancin gyaran hanyoyi da sauran ababen more rayuwa, ciki har da farfado da aikin bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK).
Har ila yau, ya yi alkawarin mayar da hankali kan samar da ruwan sha mai tsafta a yankunan karkara da birane.
A karshe, ya yi kira da a farfado da masana’antar yadi ta Kano, wadda ya ce tana da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin jihar.
Ya kara da cewa, idan aka ba shi dama, zai yi aiki tukuru wajen samar da sauyi mai ma’ana da zai amfani al’ummar Kano ta Tsakiya.
Fitowarsa takara na kara zafafa fafatawar siyasa a wannan yanki mai muhimmanci a jihar Kano gabanin zaben 2027.
