Connect with us

News

Kwankwaso Ya Ce Bai Yanke Shawara Kan Makomar Siyasarsa Ba Har Yanzu

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce har yanzu bai yanke hukunci na karshe kan makomarsa ta siyasa ko ta magoya bayansa ba, duk da rade-radin da ake yi kan yiwuwar sauya sheka daga jam’iyyar ADC.

A wata sanarwa da ya fitar, Kwankwaso ya ce akwai bayanai masu rudani da ke yawo a kafafen yada labarai dangane da matsayinsa a siyasa, musamman bayan matsalolin da ke addabar ADC.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Ta Ci Gaba Da Aikin Titin Kano-Gwarzo-Dayi Sakamakon Biyan Diyya Da Gwamnatin Abba Ta Yi

Ya bayyana cewa hukuncin kotun koli da ya tabbatar da halascin kwamitin gudanarwa na kasa karkashin jagorancin David Mark ya kuma mayar da shari’ar zuwa babbar kotu, lamarin da ya sanya jam’iyyar cikin wani yanayi mai sarkakiya.

Advertisement

Kwankwaso ya kara da cewa wata babbar kotun tarayya ta kuma soke halascin babban taron jam’iyyar na baya-bayan nan, yayin da babban lauyan gwamnatin tarayya ya nemi wata kotu ta soke rajistar ADC.

Tsohon ministan tsaron ya ce sun fice daga jam’iyyar NNPP ne saboda matsalolin shari’a da ya ce wasu na waje suka haddasa, yana mai cewa yanzu ADC ma tana fuskantar irin wannan matsala.

Advertisement

Saboda haka, ya ce shi da sauran masu ruwa da tsaki sun fara tuntubar wasu jam’iyyu da shugabanninsu ciki har da NDC da PRP domin duba mafi alherin mataki na kare muradunsu na siyasa da dimokuradiyya.

Kan batun takarar shugaban kasa kuwa, Kwankwaso ya ce bai bayyana aniyar tsayawa takara ba, kuma bai goyi bayan kowane dan takara ba. Ya tuna cewa a zaben fidda gwani na APC a 2014 ya zo na biyu bayan Muhammadu Buhari, sannan a 2019 ya nemi tikitin PDP kafin daga bisani ya mara wa Atiku Abubakar baya bayan ya lashe zaben fidda gwani.

Advertisement

Kwankwaso ya ce a kullum yana fifita hadin kan jam’iyya da muradun kasa sama da bukatun kansa.

Ya kuma bayyana cewa rashin halartarsa a tarukan masu ruwa da tsaki na ADC guda biyu da aka yi kwanan nan ya faru ne saboda wasu uzurori na kashin kai, kuma ya sanar da shugabannin jam’iyyar tun da wuri.

Advertisement

A karshe, ya ce duk wani hukunci da zai dauka game da alkiblarsa ta siyasa za a sanar da shi ne ta hanyoyin hukuma a lokacin da ya dace.

 

Advertisement

 

DCL

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending