Interview
Yan Kasuwa a Kano Sun Koka Kan Kama Kayansu da Hukumar Kwastom Keyi ba bisa Ka,ida ba
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Yan Kasuwar da ke kasuwanci a jihar Kano na Cigaba da kokawa bisa kama Kayansu da Hukumar Kwastom Keyi ba tare da wani dalili ba.
Sun bayyana cewa jami’an na Kwastom na matsa musu ta hanyar Kafa shigen bincike Masu yawan gaske a manyan Hanyoyin Fita na Jihar Kano, Musamman Titin Maiduguri da hanyar Kaduna zuwa Zaria.
Kamal Yahya Matashin dan kasuwa ne Dake Fitar da Kaya daga Jihar Kano zuwa wasu jihohi ya Bayyana cewa ko jami’an Kwastom Suna kama motocin Yan Kasuwa.
Dan Kasuwar ya Bayyana cewa jami’an sunyi ikirarin Harbin direban daya daukar masa Kaya tare da zargin kwace masa motoci da Kayan da yake kasuwanci guda 8 wanda Ya Bayyana cewa Kayan basa cikin jerin Kayan da Hukumar Hana Fasakauri ta Kwastom ta haramta shigo dasu ko Fita dasu.
Wani direba Dake dakon Kayan Yan kasuwan da yanemi a sakaye sunansa ya Bayyana Yadda jami’an Kwastom na matsa musu da karbe karben kudaden cin Hanci a hannunsu wanda suke kira da D O Inda ya ce jami’an sukan karbi naira dubu biyar zuwa dubu goma ga duk motor da suka tare.
A Karshe Kamal Yahya ya yi kira da Gwamnatin Jihar Kano Karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ta shiga lamarin don gudun tabarbarewar Harkar kasuwanci.
Duk kokarinmu na jin tabakin Hukumar Hana Fasakauri shiyar Kano da Jigawa don jin suna sane da Wannan zargi da Yan Kasuwa ke musu bamu samu damar Hakan ba
zata Amman zamu Cigaba da bibiyar Wannan lamarin Domin samun dai-dai to