Interview
Wajibi ne musulmi ya yawaita yin salati domin Fa’idoji da Falalar Salatin Annabi (SAW) —Mai Anwaru
TAMBAYA: Shin ana saka kaya a Aljanna ko kuwa yadda a ka tashi haka za a ci gaba da zama? Tare da Imam Bello Mai-Iyali
TAMBAYA: Salatin Annabi guda nawa ne?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Salatin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa Salama, daya ne daga cikin manyan Ibadu, kuma addu’a ce daga cikin addu’o’i masu amfani duniya da lahira, kuma yana daga cikin abubuwan da ke nuna cikkakiyar soyayya da girmamawa ga Annabi SAW, kuma hakki ne daga cikin hakkokan sa Sallallahu Alaihi wa Sallam.
An ruwaito sigogin salatin Annabi SAW, da yawa a cikin ingatattun Hadisan sa, Amma mafi daraja daga cikin salatin Annabi SAW, shi ne sigar da Annabi ya yayar da sahabban sa, wanda Imamul Mukhari da Muslim suka ruwaito kamar haka:
«اللهمَّ صلِّ على محمَّد وعلى آل محمَّد، كما صليتَ على إبراهيم وعلى آل
إبراهيم؛ إنَّك حميدٌ مجيد. اللهمَّ بارِك على محمَّد وعلى آل محمَّد،
كما باركتَ على إبراهيم وعلى آل إبراهيم؛ إنَّك حميدٌ مجيد».
البخاري (3370 / (مسلم (406)
Imamun Nawawi ya hada sigogin salatan a cikin wanna sigar da wasu malamai ke ganin girman darajar sa:
اللهم صل على محمد عبدك ورسولك النبي الأمي وعلى آل محمد وأزواجه وذريته
كما صليت على إبراهيم وعلى آل إبراهيم وبارك على محمد وعلى آل محمد
وأزواجه وذريته كما باركت على إبراهيم وعلى آل إبراهيم في العالمين إنك
حميد مجيد.
Babu laifi mutum ya takaita salati kamar Allahuma Sali Ala Muhammad wala Ali Muhammad, ko Sallallahu Alaihi wa Sallam da sauran gajerun lafuzzan salati.
Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salama, wajibi ne akan dukkan musulmi. An wajabta salatin ne ba tare da bada lokacin yinsa ba. Wato, ana son bawa ya yawaita yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam.
Hadisai sun ingata cewa duk wanda baya yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam, to, an turmuza hancinsa cikin wuta. A wani kaolin kuwa akace ya kuskure hanyan Al-Jannah.
GURAREN DA AKESON YIN SALATIN SALLALLAHU ALAIHI WA SALAM
1) Ana yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam bayan tahiyar karshe a cikin Sallah.
2) Ana yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam duk lokacin da aka ambaci sunan sa ko aka rubuta shi.
3) Anyi umurnin yawaita Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam duk ranar juma’a.
4) Ana yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam yayin shiga ko fita masallaci.
5) Ana yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam bayan tahiyar karshe a cikin Sallah.
6) Ana yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam bayan tahir karshe a cikin Sallah.
7) Ana yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam bayan kiran Sallah.
8) Ana yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam lokacin hudubar juma’a ko makamantan ta.
9) Ana yin Salatin Annabi Sallallahu Alaihi wa Salam kafin addu’a.
10. Dalilin samun gafara ne daga Allah.
11. Shi Salatin Annabi SAW babbar hanya ce ta samun isarwar Allah gareka akan dukkan abinda ya dameka (wato Allah zai share maka hawayenka).
12. Salatin Annabi SAW hanya ce ta samun kusanci ga Manzon Allah SAW aranar Alqiyamah.
13. Idan kayi salati agareshi SAW to Allah zai baka ladan wanda yayi sadaqah. (Musamman ga Matalauta).
14. Hanya ce ta samun biyan bukatu cikin Sauki in sha Allahu.
15. Hanya ce ta samun Salatin Mala’iku agareka da zarar kayi masa salati.
16. Hanya ce ta samun tsarkakuwar zuciyar mai yin salatin.
17. Hanya ce ta samun bisharar samun Aljannah agareka tun kafin mutuwarka.
18. Hanya ce ta samun tsira daga tashe-tashen hankulan ranar Alkiyamah.
19. Hanya ce ta samun mayar da salati da sallama agareka daga Annabi SAW.
20. Hanya ce ta samun tunawa da abinda ka manta (Wato idan ka manta da wani abu, da zarar kayi ma Annabi salati sai kaji ka tuno da abun).
21. Hanya ce ta samun kamshin wajen Zama, kuma duk wajen zaman da akayi ma Annabi salati, ba zai zama abin nadama ga Ma’abotansa ba, a ranar Alkiyamah.
22. Ta dalilin yin salati agareshi za’a cire sunanka daga layin Marowata a wajen Allah.
23. Ita hanyar tsira ne ga mai yinta, Domin Allah zai kirashi da bawansa.
24. Ita hanya ce ta samun kuɓuta daga turmuzuwar hanci ga wanda bai yi salati agareshi ba, duk sanda aka ambaceshi.
25. Salatin Annabi (saw) yana sanya mai yinsa akan Tafarkin shiga Aljannah.
Salati da aminci su tabbata agareka Ya Abal Qasimi, gwargwadon darajarka da matsayinka awajen Ubangijinka.
Albarkacin wannan salatin ya Allah ka zaunar da kasammu lafiya kuma tabbatar damu bisa tafarkinka madaidaici, tare da ‘Ya’yanmu da dukkan al-ummar musulmi. Amin.
Ya Allah muna addu,a da Kuma tawassali a gareka da Ka kawowa Al,ummar musulmim Nigeria saukin rayuwa baki daya