Interview
Rabuwar Kawunan Yan Arewa Da Ake Samu Shi Ne Babban Abin Da Ke Kawo Koma Baya —Malam Abba
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Malam Abba Adamu Koki ya ce rabuwar kawunan yan arewa da ake samu shi ne babban abin da ke kawo koma baya ga al, ummar Arewacin Najeriya.
Mala Abba Kokii ne ya bayyana hakan a yau talata yayin zantawar sa da Jaridar Inda Ranka a Kano
Cikakken Dalilin Da Yasa Aka Gurfanar Da Dan Bilki Kwamanda A Kotu
Haka zalika Malam Abba ya yi Allah-wadai da mayar da wasu sassan babban bankin Najeriya da hedikwatar hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasa FAAN daga Abuja zuwa jihar Legas.
Malam Abba ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta canja shawara tun da wuri kasan cewar hakan na barazana ga rayuwar yan Arewacin Najeriya
Majiyoyi a cikin bankin dai sun ce ana samun karuwar matan aure da ke tunanin ajiye aiki, da nufin kauce wa zuwa Ikkon da ke iya kaiwa ga rabasu da iyali.
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Babban bankin na CBN a cikin wata sanarwa da ya fitar a makon da ya gabata ya bayyana shirin mayar da wasu sassan nasa zuwa Legas saboda kasancewar hedikwatarsa da ke Abuja na cike da cunkoso na ma’aikata.
Hakazalika, ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya, Festus Keyamo shi ma ya sanar da mayar da hedikwatar FAAN daga Abuja zuwa Legas.
Bayan tsawon lokaci daga dukkan alamu ana shirin fuskantar takun saka tsakanin gwamnatin Najeriya da dattawan arewacin kasar bisa shirin mayar da wasu ma‘aikatu da hukumomin gwamnati zuwa birnin Ikko.