Interview
Rashin sana’a ga matasa ne matsalar Nijeriya -Muhammad Zahraddin
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wani dan jarida da ke Jihar Kano. Muhammad Muhammad Zahraddin , ya nuna matuƙar damuwarsa da yadda yara matasa ke yawo a kan tituna, ba tare da koyon wata sana’a ba.
A wata tattaunawa da wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi a kano
Magoya Bayan Jam’iyyar Labour Party Sun Gudanar da Zanga-Zanga a Ofishin INEC
Ya ci gaba da cewar, rashin samar da sana’o’in ga matasan Nijeriya musamman matasan da suke Arewa wannan a cewarsa shi ya haifar da matsalolin tsaro da ya addabi kowa musamman a Arewacin Nijeriya.
A nan ne Muhammad ya shawarci duk wanda yake da sana’ar hannu ya fara tunanin makomar matasan Nijeriya a zuciyarsa.
Ya ƙara da cewar rashin sa ido ga yara su samu sana’ar da zai tallafa wa rayuwarsu na kan gaba, na matsalolin da suka zama silar ƙamfar tsaro a Arewa za su zama tarihi a ɗan lokaci kaɗan.
Haka kuma ya tabbatar da cewar matuƙar aka ƙara sa ido na ganin yara sun samu sana’ar da za su rayu har su tallafa wa wasu matsalolin tsaro a Arewa za su zama tarihi a lokaci kaɗan.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
