Connect with us

Interview

Ba iya karatu muke koyar da Dalibai ba har da zamantakewar Yau Da Kullun -Dakta Sabo Wada Dutse.

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Shugaban kwalejin kimiyya da fasaha ta Hussaini Adamu Dake kazaure a jihar jigawa Dakta Sabo wada Dutse, yace ba’a iya karatun boko suke koyar da Dalibai ba harda yadda zasuyi mu’amulla da juna tare da kulawa da tarbiyyar Daliban kwalejin kasancewar kwalejin ta hada mutane daga jihohi maban banta a addini da yare dakuma alada na fadin Najeriya.

Advertisement

 

Ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake kwalejin kimiyya da fasaha ta Hussaini Adamu Dake kazaure

Rundunar Sojoji sun gano wurin haɗa bindiga a  jahar Kaduna

Haka kuma yace “Duba da kwalejin na karkashin gwamnatin tarayya Dukkanin Daliban kasarnan nada damar neman Gurbin karatu a kwalejin a shirye muke tsaf wajen bada gurbin karatu a kwalejin domin karantar ilimin kimiyya da fasaha wanda idan har Dalibi yakaranta to babu shakka zai iya dogara dakansa batare da yajira aikin gwamnati ba ko kuma wani Dalibi nada damar amfani da iliminsa na kimiyya wajen gudanar da sana’oi iri iri domin ka samu ingantacciyar rayuwa”.

Advertisement

 

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Dakta sabo wada yakara da cewar “Ina janhankali ga Daliban wannan makarata dasu zamo masu mutumta juna dukda banbancin yare da addini da kuma alada kowa yake mutumda addinin kowa kada Dan Arewa yake kyamatar Dan kudu ko Dan kudu yake kyamatar Dan Arewa mudauka cewar tunda karatu yahada mu to muzamo tsintsiya daya madauri daya.

 

Advertisement

Sannan Ina kara jan hankalin Dalibai dasu mayarda hankali wajen karatunsu domin ilimi shine jigon rayuwa duba da mashimmancin sa ga rayuwar mu, kada Makaranta tazamo gurin da muke aikata badai dai ba muyi amfani da lokacin mu wajen ginawa kan mu gobe mai kyau, kada muzamo masu cin amanar iyayen mu akan abinda suka turomu mu koya.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *