Connect with us

News

Yan-sanda Sun Kama Magidanci Da Ya Kashe Matarsa Kan Abincin Buda Baki A Bauchi

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Rundunar ‘yan-sandan jihar Bauchi ta cafke wani dan kasuwa mai suna Alhaji Nura Isa, mai shekaru 50, bisa zargin kashe matarsa ta biyu Wasila Abdullahi mai shekaru 24, sakamakon sabani da suka samu kan abincin buda baki na Azumin Ramadan.

Jaridar NIGERIAN JOURNAL ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne jiya da yamma a unguwar Fadamar Mada cikin garin Bauchi, daidai lokacin da ake shirin bude baki.

Bincike ya nuna cewa, rikicin ya fara ne kan rabon kayan abinci, inda magidancin ya dauki bulala ya dinga dukan matar har sai da ta suma. Bayan haka ne ‘yan sanda suka kai ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), inda Likitoci suka tabbatar da rasuwarta.

Advertisement

A halin yanzu, gawar mamaciyar na ajiye a dakin ajiyar gawa, yayin da mijinta ke hannun ‘yan sanda a sashin binciken kisan kai na State CID Bauchi.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Bauchi, CP Auwal Musa Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da alkawarta gudanar da bincike na gaskiya da kuma gurfanar da wanda ake zargi a gaban Kotu ba da jimawa ba.

 

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *