News
Gwamnatin Kano Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Magance Ciwon Hawan Jini a Cibiyoyin Lafiya 208
Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta fadada ayyukan rigakafi da kula da ciwon Hawan Jini zuwa cibiyoyin lafiya 208 a fadin jihar. Wannan ci gaba na zuwa ne domin yaki da cutar da ke daga cikin manyan dalilan da ke haddasa ciwon zuciya, bugun jini, gazawar koda da mace-mace da wuri a Najeriya.
Gwamnatin ta bayyana cewa cibiyoyin lafiya na matakin farko sune wurin farko da jama’a ke samun kulawar lafiya, don haka aka kara karfafa ayyukan rigakafi da kula da ciwon Hawan Jini domin kusantar da kulawa ga al’umma.
A matakin farko na shirin, an fara ayyukan a cibiyoyin lafiya 52 karkashin Shirin Kasa na Kula da Ciwon Hawan Jini (NHCI) tare da hadin gwiwar kungiyoyin Resolve to Save Lives da Project HOPE. A nan, ana gudanar da duba jini na yau da kullum, fara magani da kuma bibiya ga masu fama da cutar.
Bayan nasarar wannan mataki, gwamnati ta fadada shirin zuwa cibiyoyin lafiya 208 a cikin kananan hukumomi 44 na jihar. Wannan zai bai wa dubban mazauna jihar damar gano cutar tun da wuri, fara magani da samun bibiya a cikin al’umma ba tare da wahala ba.
Kwamishinan Lafiya, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya yabawa ma’aikatan lafiya da ke cikin shirin tare da kira gare su da su ci gaba da jajircewa domin tabbatar da dorewar nasara wajen yaki da ciwon Hawan Jini.
Gwamnatin ta ce wannan mataki zai zama abin koyi ga sauran jihohi a Najeriya wajen inganta kulawar lafiya da rage mace-mace sakamakon cututtuka marasa yaduwa.
