Connect with us

News

Jami’an Kwastam Ta Ƙwace Sama Da Lita 34,000 Na Fetur Da Aka Yi Safararsa A Taraba

Published

on

customs riffle

Hukumar hana fasa kwauri a Najeriya ta ce jami’anta na Operation Whirlwind sun ƙwace litar man fetur 34,470 wanda aka yi safararsa a jihar Taraba, a ƙoƙari da take yi wajen yaƙi da masu safarar mai

Babban Kwanturola na hukumar ta kwastam, Bashir Adewale ne ya sanar da haka ga manema labarai a Jalingo, inda ya ce sun samu nasarar ce a garin Gembu na karamar hukumar Sardauna a jihar da kuma Kan-Iyaka da ke makwabtaka da ƙasar Kamaru.

Advertisement

Hanyar da ta bi Kan-Iyakar dai ta kasance gungun wuri da aka fi safarar man fetur zuwa waje.

Gwamnatin Kano Ta Yi Allah-wadai da Rashin Bayyana Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara Kan Rikicin Masarauta

Adewale ya ce sun kuma ƙwace wata babbar mota dakon kaya da aka yi amfani da ita wajen safarar mai ɗin, inda ya ƙara da cewa sun kai samamen ne tare da haɗin gwiwar hukumar kula da sarrafawa da kuma tace man fetur (NMDPRA) da kuma taimakon ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro.

Advertisement

“Mun ƙwato jarakuna mai 1,149 – kowane yana ɗauke da lita 30, abin da ya tashi zuwa lita 34,470,” in ji Adewale.

Ya ce masu safarar barazana ne ga tsaron ƙasar kuma ya zama wajibi a kama tare da hukunta su.

Advertisement

Ya yi kira ga mazauna jihar da su bai wa gwamnati haɗin-kai domin tabbatar da ganin cewa an kakkaɓe ɓata-garin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending