News
Gwamnatin Kano Ta Yi Allah-wadai da Rashin Bayyana Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara Kan Rikicin Masarauta
Gwamnatin Jihar Kano ta nuna damuwa kan rashin bayyana hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke dangane da rikicin masarautar Kano.
A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, gwamnati ta umarci lauyoyinta da su yi nazarin umarnin kotun da aka bayar a ranar Juma’a, tare da ɗaukar matakin da ya dace da doka.
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Watsi Da Bukatar Kafa Sabbin Jami’o’i 200
Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Haruna Dederi, ya bayyana cewa hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na ranar 10 ga watan Janairu ya tabbatar da soke dokar masarautun Kano ta 2019, tare da soke hukuncin babbar kotun tarayya da ke Kano.
“Da Alhaji Aminu Babba Ɗan’agundi ya ga bai gamsu da hukuncin ba, sai ya garzaya zuwa kotun ƙoli,” in ji Dederi. Ya kuma jaddada cewa hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na farko yana nan daram, har sai kotun ƙoli ta yanke nata hukuncin.
Gwamnatin Kano ta bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin lumana, yayin da take godiya ga ‘yan jihar bisa haƙurinsu da addu’o’in da suke yi domin zaman lafiya a jihar da ƙasa baki ɗaya.
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News5 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
