Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Watsi Da Bukatar Kafa Sabbin Jami’o’i 200

Published

on

 

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi watsi da bukatar majalisun dokokin tarayya na kafa sabbin jami’o’i guda 200, tana mai cewa abin da ya fi dacewa shi ne inganta jami’o’in da ake da su a halin yanzu.

Advertisement

Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ministoci ke shiryawa, wanda aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja. Ya ce Najeriya na da jami’o’i 278, inda 64 ke karkashin Gwamnatin Tarayya, 67 na jihohi, yayin da 147 ke zaman kansu.

Ba Sauya Jam’iyya Ke Da Muhimmanci Ba, Sai Sauya Gurbataccen Tunani Don Ceto Arewacin Najeriya 

A cewarsa, jami’o’in masu zaman kansu na iya daukar dalibai 875,000 kacal, wanda ke wakiltar kaso 7.5% na jimillar daliban jami’o’in kasar. Ministan ya kara da cewa, “Yanzu abin da ke gaban gwamnati ba kirkirar sabbin jami’o’i ba ne, sai dai kula da ingancin wadanda ake da su.”

Advertisement

Wannan mataki na gwamnati ya janyo cece-kuce daga wasu ‘yan Najeriya da ke ganin bukatar kara yawan jami’o’i don rage cunkoso da samar da karin guraben karatu ga matasa.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending