Connect with us

News

A Kan Dubu Uku Mutum Yana Iya Mutuwa A Asibiti A Najeriya  —Fauziyya D. Sulaiman

Published

on

images

Fitacciyar mai aikin jinƙai a Arewacin Najeriya, Fauziyya D. Sulaiman, ta bayyana damuwarta kan yadda rashin kuɗi ke haddasa asarar rayuka a asibitocin ƙasar.

A wata tattaunawa da ta yi da TRT Afrika Hausa, ta bayyana cewa akwai marasa lafiya da ke rasa rayukansu saboda ƙarancin kuɗi, har ma da adadin da bai wuce naira dubu uku ba.

Advertisement

Jami’an Kwastam Ta Ƙwace Sama Da Lita 34,000 Na Fetur Da Aka Yi Safararsa A Taraba

Fauziyya ta kuma yi bayani kan ƙalubalen da kungiyarta ke fuskanta wajen bayar da tallafi, musamman bayan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan rabon likkafani da suka yi a Kano.

Ta ce manufarsu ita ce taimakawa jama’a da rage musu wahala, ba ƙara tsananta matsalolinsu ba.

Advertisement

Duk da ƙalubale da sukar da suke fuskanta, ta jaddada cewa za su ci gaba da tallafawa mabukata, musamman a fannonin kiwon lafiya, abinci da kayan masarufi.

Mazauna da dama sun nuna goyon bayansu ga irin namijin ƙoƙarin da take yi, suna mai cewa irin waɗannan ƙungiyoyi na taka muhimmiyar rawa wajen rage radadin wahala a cikin al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending