Connect with us

News

Kwamitin Tabbatar Da Tsaro A Kano Ya Kaddamar Da Gagarumin Samame Kan ‘Yan Daba Da Masu Shaye-shaye

Published

on

IMG 20250315 WA0024

 

Kwamitin tabbatar da tsaro a Jihar Kano kan Farfado da Zaman Lafiya da Gyaran rayuwar Matasa, karkashin jagorancin Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata, ya kaddamar da gagarumin samame a wasu yankunan birnin Kano, inda aka kama mutum 53 da ake zargi da laifukan fashi, shaye-shaye da safarar miyagun kwayoyi.

Advertisement

A cikin sanarwar da Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Kwamitin, ya fitar ranar Asabar, ya bayyana cewa, samamen da aka gudanar tsakanin 13 zuwa 14 ga Maris, 2025, ya shafi yakin Yakasai, Kofar Mata, Zango, Zage, Zanzado, Rimi Market, Shahuchi Park, Kano Line, Sharada, Ja’en, Dan Agundi da kewaye.

A Kan Dubu Uku Mutum Yana Iya Mutuwa A Asibiti A Najeriya  —Fauziyya D. Sulaiman

A yayin aikin, jami’an tsaro sun samu nasarar kwace:

Advertisement

Kwayoyin Wiwi: Parcels 3, rufe 50 da wasu dimbin busassun ganyen da ake zargin cannabis sativa ne.

Magungunan Maye: Robobi 2 na Codeine, tubuna 2 na turaren Sholisho, gallan 1 na Suck and Die, da kwallaye 105 na Exol Tablets.

Advertisement

Muggan Makamai: Adduna 5, almakashi 2, sanduna 2 (Gora) da wata tarin tsafi.

Haka kuma, an samu babbar ganima a sansanin miyagun kwayoyi na Zanzado, inda aka kwace tarin ganyen Wiwi. Baya ga haka, an kama wata motar dakon kaya da shanu 5 da ake zargin mallakin wani shahararren mai safarar miyagun kwayoyi ne.

Advertisement

Sanarwar ta kara da cewa duk wadanda aka kama za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike. Wannan samame dai wani muhimmin ci gaba ne a yunkurin Kano State Joint Task Force Committee na yaki da ayyukan fasiqanci da shaye-shaye a Jihar Kano.

Kwamitin ya jaddada aniyarsa ta inganta zaman lafiya da tsaftace titunan Kano daga miyagun ayyuka, tare da tabbatar da lafiya da tsaro ga al’ummar Jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending