News
Masu Tauna Cingam Na Haɗiye Ƙananan Robobi Ba Tare Da Sun Sani Ba – Masana
Wani sabon bincike da masana kimiyya suka gudanar ya gano cewa masu tauna cingam na hadiye dubban ƙananan robobi ba tare da sun sani ba, abin da ka iya haifar da illa ga lafiyarsu.
Rahoton ya nuna cewa waɗannan robobi suna iya makalewa a cikin huhu da kwakwalwar bil’adama. Sanjay Mohanty, shugaban tawagar binciken daga Jami’ar California, ya bayyana cewa sun gano sinadaran roba kusan 100 a yawun mutanen da suka ci cingam.
Masana sun bukaci a ƙara wayar da kan jama’a game da haɗarin sinadaran da ke cikin cingam, tare da kira ga kamfanonin sarrafa shi da su bayyana sinadarai da suke amfani da su.
Duk da haka, manyan kamfanonin cingam, kamar Wrigley, ba su yi tsokaci kan binciken ba.
Advertisements
