News
Dakarun Sojin Najeriya Guda 200 Zasu Samu Horo A Turkiyya
Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin aikewa da jami’an tsaron ƙasar na musamman aƙalla 200 don samun horo a Turkiya ƙarƙashin wata yarjejeniya da ɓangarorin biyu suka cimma, wadda za ta fara aiki cikin gaggawa.
Ministan tsaron Najeriyar Janar Christopher Musa mai ritaya ne ya sanar da wannan mataki bayan tattaunawarsa da takwaransa na Turkiyya Yasar Guler a wani ɓangare na taron diflomasiyyar ƙasar ko kuma Antalya Diplomacy Forum karo na 5 da ya gudana jiya Asabar.
An Ceto Daliban Da Aka Sace A Hanyar Zuwa Jarrabawar JAMB
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa taron na kwanaki 3 ne kuma ana saran halartar ɓangarorin tsaro daga ƙasashe da dama wanda za a yi ƙawance da Turkiyya haɗa ƙarfi don tunƙarar matsalolin tsaro.
Ministan tsaron na Najeriya ya yi bayanin cewa da zarar an kammala taron ne jami’an tsaron Najeriyar na musamman za su isa Ankara don fara karɓar horon bisa buƙatar hakan daga Turkiya
Ministan ya ci gaba da cewa baya ga wannan horo na jami’ai 200 akwai sauran yarjeniyoyin taimakon juna tsakanin Najeriyar da Turkiya a ɓangaren tsaro inda ƙasashen biyu za su ci gaba da aiki tare.
Christopher Musa ya kuma ce Najeriyar da Turkiyya sun amince da haɗa ƙarfi wajen ƙirar wasu kayakin yaƙi da kuma musayar fasaha a ɓangaren tsaro.
Akwai dai alaƙa mai ƙarfi tsakanin Najeriyar da Turkiyya wadda ta faro tun shekarun 1960.
Haka zalika kamar yadda Najeriya ke fama da matsalolin ta’addanci na kusan shekaru 17, itama Turkiya na fuskantar matsananciyar matsalar ta shekaru 40 batun da Christopher Musa ke cewa bisa ga gogewar ƙasar ta Turai ko shakka babu za ta taimakawa Najeriyar wajen magance na ta matsalolin da suka dabaibayeta.
