Connect with us

News

Masu Kwacen Waya Sun Kashe Ɗalibin BUK A Kano

Published

on

buk new 3

Wasu masu kwacen waya sun daba wa ɗalibin shekara ta uku na Jami’ar Bayero Kano (BUK), Umar Abdullahi Hafizi, wuka har lahira a unguwar Dorayi, ƙaramar hukumar Gwale a Kano.

Lamarin ya faru misalin ƙarfe 11 na dare, inda ya jefa al’ummar jami’ar cikin alhini da jimami.

Advertisement

 

Jami’an Kwastam Sun Kama Tankar Mai Dauke Da Buhunan Shinkafa A Kaduna

Jami’ar ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga al’ummarta, inda ta tabbatar da cewa tana aiki tare da jami’an tsaro domin cafke masu laifin.

Advertisement

 

 

Advertisement

Shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya ce jami’ar na ƙoƙarin ganin an hukunta masu hannu a kisan.

Jami’ar ta yi kira ga ɗalibai da su kwantar da hankali tare da bada hadin kai wajen samar da bayanan da za su taimaka ga bincike.

Advertisement

A ƙarshe, BUK ta roƙi Allah ya jikansa, tare da baiwa iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending