News
EFCC Ta Gurfanar da Jami’an Haraji Biyar da Ma’aikacin Banki A Kotu Bisa Zargin Wawure Naira Biliyan 1.2 A Katsina
Hukumar EFCC ta shigar da ƙarar wasu jami’ai biyar na hukumar tara haraji ta jihar Katsina da kuma wani ma’aikacin banki a gaban babbar kotun jihar bisa zargin karkatar da kudaden jama’a da suka kai fiye da Naira Biliyan 1.2.
An gurfanar da su ne a ranar Talata, 5 ga watan Agusta, 2025, a gaban Mai Shari’a Musa Danladi na Babbar Kotun Katsina, bisa tuhumomi bakwai da suka haɗa da haɗin baki wajen karkatar da kuɗin haraji na gwamnati.
EFCC ta bayyana cewa kuɗaɗen sun fito ne daga kungiyoyin agaji na ƙasashen waje – Médecins Sans Frontières (MSF) da kuma ALIMA – waɗanda aka biya gwamnatin jihar Katsina, amma suka shiga hannun waɗanda ake zargi ba bisa ƙa’ida ba.
Waɗanda ake tuhuma sun haɗa da, Nura Lawal, Sanusi Mohammed Yaro, Ibrahim Mamman, Abubakar Saidu, Rabiu Adamu Abdullahi
Adam Alhassan Albashir – wanda EFCC ta bayyana da cewa shi ne Manajan Hulɗa da Jama’a na Bankin First Bank.
EFCC ta ce laifin ya faru ne tsakanin watan Janairu 2022 zuwa watan Agusta 2024, inda wadanda ake zargin suka karkatar da kudaden haraji da ya kamata a tura wa gwamnatin jihar, suka mayar da su amfanin kansu.
A cewar takardar tuhuma, hakan ya saba wa Sashe na 58 na Penal Code na Jihar Katsina, kuma hukuncin sa na karkashin Sashe na 298.
Dukkan wadanda ake tuhuma sun musanta laifukan da ake zarginsu da su a gaban kotu.
Lauyan EFCC, Musa Isah, ya roƙi kotun da ta dage shari’ar domin samun damar gabatar da shaida da kuma tabbatar da zargin.
Sai dai kowanne daga cikin lauyoyin da ke kare wadanda ake tuhuma ya nemi beli ga wanda yake karewa, inda suka ce wadanda ake zargin ba za su gudu ba, kuma za su tsaya tsayin daka har zuwa ƙarshe na shari’ar.
EFCC ta nuna rashin amincewa da buƙatar belin, tana mai cewa akwai yiwuwar hakan ya kawo cikas ga bincike da shari’a.
Bayan sauraron ɓangarorin biyu, Mai Shari’a Danladi ya bayar da beli ga kowanne daga cikin wadanda ake zargi a kan kudi Naira Miliyan Biyar (₦5,000,000), tare da sharuɗɗa masu tsauri. Ciki har da samar da mai tsaya musu guda ɗaya da ke zaune cikin ikon kotu, kuma mai kadarar ƙasa wacce za a tabbatar da ita ta hannun mai rajistar kotu.
An dage cigaba da sauraron ƙarar zuwa ranar 27 ga Oktoba, 2025.
