News
Rundunar Sojin Sama Ta Kai Hari Gurin Shagalin Auren Yan Bindiga A Zamfara
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta kai wani hari ta sama kan wani taron biki da ake zargin na ‘yan bindiga ne, a tsaunukan Asaula da ke cikin ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Rahotanni daga yankin sun tabbatar da cewa an kai harin ne da misalin ƙarfe 4:00 na yamma ranar Talata, lokacin da ‘yan bindigar suka hallara domin bikin aure, wanda ya haɗa mayaka daga jihohin Zamfara da Katsina.
Wata majiya mai tushe daga Zagazola Makama, wata kafar da ke bibiyar al’amuran tsaro a yankin Arewa maso Yamma da Tafkin Chadi, ta ce jirgin yaki ya samu nasarar hallaka wasu daga cikin ‘yan bindigar, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Bikin, wanda aka ce ya tara manyan ‘yan bindiga daga sassa daban-daban na Zamfara da Katsina, ya kasance wani babban taro ne da harin ya tarwatsa.
Operation Fansar Ƴan Bindiga, wanda rundunar soji ta ƙaddamar a farkon wannan shekarar, na ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin ‘yan bindiga da wuraren ɓoyarsu a jihohin Zamfara, Katsina, Kebbi da Sokoto.
Kakakin rundunar sojin sama bai fitar da sanarwar hukuma a hukumance ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
-
News22 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
