News
Gamayyar kungiyoyin APC 12 Sun Bayyana Goyon Bayansu Kan Sauya Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano

Gamayyar kungiyoyin Jam’iyyar APC na jihar Kano sun fito fili wajen bayyana goyon bayansu ga matakin da Gwamna ya dauka n bukaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta sauya kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, bisa zarginsa da rashin kwarewa da kuma yin aiki ba bisa ƙa’ida, bayan janyewar yan sanda daga bukin cikar shekaru 65 na samun ‘yancin kai.
Kungiyoyin sun hada da Kano State APC Integrity Group, APC Amalgamation Forum, APC Intellectual Forum, Ganduje Support Group, APC Concern Forum, APC Media Enlightenment Forum, Abdullahi Abbas Political Vanguard, Tinubu/Shettima Political Movement, Kano State APC Mager, APC Kano Central Movement, Gawuna/Garo Political Awareness da APC Dan Sarki Organization.
A cikin sanarwa da suka fitar ga manema labarai, kungiyoyin sun bayyana cewa:
”Mun shirya wannan ganawa domin bayyana matsayinmu kan abubuwan da ke faruwa a jihar. Mun goyi bayan kiran Mai Girma Gwamna na daukar matakin shugabancin yan sanda bayan janyewar yan sanda daga bikin.”
Kungiyoyin sun kuma yi gargadi kan duk wani yunkuri na siyasantar da harkar tsaro ko masarauta, inda suka ce:
”Duk wani yunkuri na amfani da sunan al’umma wajen rura wutar rikici ba shi da dacewa. Mun yanke shawarar bayyana wannan matsayi ne domin kare zaman lafiya da hadin kai a jihar.”
A karshe, sun kara da cewa duk ‘yan jam’iyyar APC da shugabannin jam’iyyar jihar su tabbatar da cewa harkokin siyasa ba za su shafi tsaro da kwanciyar hankali na al’umma ba, domin ci gaban jihar Kano gaba ɗaya.