News
Mutane 2 Cikin 11 Na Fuskantar Yunwa A Najeriya — Rahoto

Masana harkar noma sun ce mutane biyu cikin kowace goma sha ɗaya (2/11) a Najeriya na fama da yunwa a kullum, yayin da ɗaya cikin biyar na nahiyar Afirka ke fuskantar ƙarancin abinci.
Wannan rahoto ya fito ne daga Onijighogia Emmanuel, wakilin shirin Comprehensive Africa Agriculture Development Programme (CAADP), a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja kan aiwatar da Yarjejeniyar Kampala ta Tarayyar Afirka.
Gamayyar kungiyoyin APC 12 Sun Bayyana Goyon Bayansu Kan Sauya Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano
Yarjejeniyar, wadda shugabannin ƙasashen Afirka suka amince da ita a Janairu 2025, na da nufin sauya tsarin noma da samar da abinci a nahiyar cikin shekaru goma masu zuwa (2026–2035).
Emmanuel ya bayyana cewa kashi 58% na al’ummar Afirka ke fama da matsananciyar rashin abinci, inda fiye da miliyan 924.8 ba sa samun abinci mai gina jiki. A Najeriya kuwa, kusan gidaje shida cikin goma ba sa iya samun abinci mai kyau.
Ya ce sama da mutane 50,000 a Najeriya na kamuwa da cututtuka duk shekara saboda cin abinci mara tsabta. Duk da cewa ƙasashen Afirka sun yi alkawarin ware kashi 10% na kasafin kuɗinsu ga harkar noma, Najeriya tana kashe kusan kashi 3% kacal.
Sai dai Emmanuel ya yaba da ƙoƙarin Ma’aikatar Noma wajen kafa kwamiti na musamman don tsara sabon shirin ci gaban noma na shekaru goma masu zuwa.
A nasa jawabin, Azubike Nwokoye na ƙungiyar ActionAid ya jaddada muhimmancin bin doka da gaskiya wajen aiwatar da yarjejeniyar Kampala. Ya bukaci gwamnati ta samar da bashin noma, ta inganta kayan aiki, ajiya da sarrafa amfanin gona, tare da shigar da mata da matasa cikin harkokin noma.
Haka nan, Grace Oyediji, shugabar ƙungiyar ƙananan manoman mata, ta roƙi gwamnati ta ƙara saka hannun jari a fannin noma da sauƙaƙa hanyoyin samun bashi.
“Manoma ba sa son yin yajin aiki, domin idan muka tsaya, babu wanda zai ci abinci,” in ji ta.
Rahotanni sun nuna cewa Najeriya na cikin mummunan halin talauci, inda fiye da mutane miliyan 133 ke fama da rashin abinci, ruwa, ilimi da kula da lafiya — matsalar da ta tsananta bayan cire tallafin mai da kuma daidaita naira a shekarar 2024.