News
Mutum 5 Sun Rasu Yayin Da Tirela Ta murƙushe Adaidita Sahu

Mutane biyar ne suka mutu a daren Juma’a a karamar hukumar Yewa South, jihar Ogun, sakamakon haɗarin mota da ya faru a kan titin Papalanto–Ilaro.
Binciken farko ya nuna cewa motar Dangote Cement ce ta Murƙushe Adaidita Sahun da mutanen suka ke ciki, inda dukkan fasinjojin suka rasa rayukansu nan take.
Ruwan Sama Ya Lalata Gadoji Da Hanyoyi A Filato, Taraba Da Kebbi Da Wasu Jihohi
Babatunde Akinbiyi, mai magana da yawun Hukumar Kula da Zarga-zargar Ababen Hawa ta Jihar Ogun (TRACE), ya tabbatar da aukuwar haɗarin da misalin karfe 8:25 na dare.
Shaidu sun bayyana cewa direban motar bai lura da haɗarin ba har sai lokacin da tayar motar ta murƙushe adaidita Sahun da mutanen ke ciki, abin da ya yi sanadiyyar mutuwarsu.
Gawarwakin an kai su dakin ajiye gawarwaki na Hukumar Kiyaye Hanyoyi ta Tarayya (FRSC) domin gudanar da bincike da shirya jana’iza.