Connect with us

News

Ruwan Sama Ya Lalata Gadoji Da Hanyoyi A Filato, Taraba Da Kebbi Da Wasu Jihohi

Published

on

Vehicles and passengers inside ferries on Namnai river near the collapsed Namnai bridge in Taraba State
Spread the love

Al’ummomi a sassa daban-daban na Najeriya na fama da mummunan tasirin ambaliyar ruwa, wadda ta lalata gadoji da hanyoyi, ta hana zirga-zirgar mutane da kaya, tare da ƙara wahalhalu ga jama’a.

Binciken Jaridar Daily Trust ya nuna cewa yawancin waɗannan gadaje sun dade ba tare da gyara mai ɗorewa ba kafin su rushe.

A Jihar Filato, rushewar Gadar Kufai da ke kusa da ƙauyen Yelwa a ƙaramar hukumar Shendam ta jefa al’umma cikin halin ƙunci. Gadar, wadda aka gina shekaru fiye da 30 da suka wuce, tana da matuƙar muhimmanci wajen haɗa zirga-zirgar matafiya da masu safarar kaya daga Filato zuwa jihohin Nasarawa da Taraba. Manyan motoci masu ɗaukar kayan abinci zuwa Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma ma na amfani da gadar.

Gadar ta fara nuna alamun rushewa tun 2022, inda aka yi mata ɗan gyaran wucin-gadi a bana, amma ruwan sama mai ƙarfi a watan Agusta ya sake wanke ta gaba ɗaya.

Advertisement

“Rushewar wannan gada ya jefa mu cikin matsala sosai. Muna kira ga gwamnati ta gyara,” in ji Wayu Bamga, ɗaya daga cikin mazauna yankin.

A Jihar Taraba, Gadar Namne ta rushe tun Agustan 2024. Duk da alƙawarin da Gwamna Agbu Kefas da NEDC suka yi, babu wani gyara da aka fara. Matafiya yanzu suna amfani da kwale-kwale don tsallaka kogin, yayin da ƙananan motoci da babura kawai ke iya bi.

“Farashin sufuri da kayan masarufi ya tashi saboda doguwar hanya da direbobi ke bi. Tsallaka kogin da kwale-kwale na da hatsari, musamman ga waɗanda ba su saba ba,” in ji wani mazaunin yankin.

A jihohi irin su Kebbi, Kogi da Neja, ambaliyar ruwan ta lalata gadoji da hanyoyi, ta katse alaƙa tsakanin ƙauyuka da birane, tare da jawo cikas ga harkokin kasuwanci da tattalin arziki.

Advertisement

 

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *