Connect with us

News

Ramadan: Farashin Ƙwai Ya Yi Tashin Gwauron Zabi A Kano

Published

on

Eggs Crates

Yayin da ake gudanar da azumin watan Ramadan, iyalai da dama a Kano na fuskantar ƙarin ƙalubalen rayuwa sakamakon tashin gwauron zabi da farashin ƙwai ya yi a kasuwanni daban-daban na jihar.

Rahoton da Daily News 24  ya nuna cewa farashin akwati na ƙwai ya kai har Naira 9,000 a wasu kasuwanni — bayan da a baya ake sayar da shi kusan Naira 5,500 kacal. Wannan tashin farashi ya faru ne cikin kwanaki shida kacal, abin da ake kallon sa a matsayin ɗaya daga cikin mafi girman hauhawar farashi a baya-bayan nan.

Advertisement

Hassada Da Rashin Haɗin Kai Ne Ke  Hana Arewacin Najeriya Ci Gaba —Alhaji Shehu Ashaka

Masana na ganin tsadar ƙwai na ƙara faɗaɗa gibin samun abinci mai gina jiki, musamman ga iyalai masu ƙaramin ƙarfi da matsakaicin hali, a lokacin da ake bukatar abinci mai sauƙin samu don buda baki.

Advertisement

Wasu mazauna birnin sun bayyana cewa tsadar ta tilasta musu rage cin ƙwai ko ma daina sayensa gaba ɗaya. Wata mata  ta ce a baya tana iya tura a sayo ƙwai uku da Naira 1,000 a dawo da ɗan canji, amma yanzu hakan ya gagara, lamarin da ya sa ta hakura da sayen ƙwai na ɗan lokaci.

Bincike da aka gudanar a Kasuwar Rimi ya nuna cewa wasu shaguna sun rasa ƙwai gaba ɗaya, yayin da masu saye ke jiran motoci masu kawo kaya ba tare da tabbacin zuwansu ba.

Advertisement

Masu sayarwa sun danganta wannan matsala da raguwar kaji masu yin ƙwai, da kuma yawaitar buƙata da ake samu a watan Ramadan.

A halin yanzu, tuni farashin nama da kifi ya yi tashin gwauron zabi, yayin da tsadar ƙwai ke ci gaba da takaita zaɓin abinci ga iyalai masu ƙaramin ƙarfi — lamarin da ke ƙara matsa lamba ga al’umma a wannan lokaci na ibada.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending