Connect with us

News

Fashin Offa: Ofishin Mai Shigar Da Ƙara Ya Wanke Saraki Tun 2018 

Published

on

Biyo bayan sake dawo da maganar fashin bankuna na Offa da aka yi a jihar Kwara wadda gwamnatin jihar Kwara ta dawo da maganar Sabuwa. Bayanai sun nuna yadda tun farko ofishin shigar da ƙara na ofishin alƙalin-alƙalai na tarayya ya wanke tsohon shugaban majalisar dattawa ta ƙasa Dr Abubakar Bukola Saraki daga zargin cewa akwai sa hannunsa a ciki.

Wasu bayanai da suke fitowa sun bayyana dalilin da ya sa Daraktan Hukumar Shigar da Ƙara ta Tarayya (DPP), Etsu Umar Mohammed, ya wanke Dr. Abubakar Bukola Saraki, daga zargi kan fashin da aka yi a Offa a shekarar 2018.

Advertisement

Kashi 7 Cikin 100 Na Kudin Sayen Makamai Kacal Aka Damka Wa Sojoji A 2025 —Rahoto

Bayanan na zuwa ne bayan da gwamnatin jihar Kwara ta shigar da sabbin tuhume-tuhume a Babbar Kotun jihar dake Ilorin kan Saraki da wasu mutane dangane da lamarin.

Advertisement

Rahotanni sun nuna cewa ofishin shigar da ƙara na tarayya ya yi nazari ne kan rahoton ‘yan sanda mai shafi 16 da DCP Abba Kyari ya jagoranta, wanda ya kunshi bincike kan harin fashi da aka kai bankuna a ranar 5 ga Afrilu, 2018 a Offa, dake jihar Kwara.

A cikin rahoton farko mai kwanan watan 22 ga Yuni, 2018, ofishin mai shigar da ƙara na tarayyaya bayyana cewa babu hujjar da ke danganta Saraki da laifukan da ake zargi, inda ya ba da shawarar a ci gaba da bincike.

Advertisement

Bayan sake samun wani rahoto daga ‘yan sanda a watan Yuli, 2018, ofishin shigar da ƙara na tarayya ya sake jaddada matsayinsa a cikin wata shawarar doka da ya fitar a watan Agusta, yana cewa babu wata hujja ta farko da ke nuna Saraki na da hannu a laifukan hada baki, fashi da makami da kuma kisan kai.

Sai dai ya bada shawarar gurfanar da wasu mutane shida da ake zargi da hannu a lamarin.

Advertisement

A yayin shari’ar, wasu daga cikin wadanda ake zargi sun ce an tilasta musu su danganta Saraki da laifin, inda suka ambaci alkawuran kudi da biza da aka yi musu domin gudawa ƙasashen waje.

Daga bisani, kotu ta same su da laifi, kuma kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin, yayin da ake jiran hukunci na ƙarshe daga kotun kolin Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending