Connect with us

Politics

Hon.sha’aban Ya Jaddada Janye Neman Takarar Sanatan Kaduna Ta Arewa, Tare Da Bayyana Goyon Duk Wanda Apc Ta Tsayar  

Published

on

IMG 20260421 WA0007

Honarabul Sani Sha’aban ya janye daga neman takarar kujerar Sanata a shiyyar Kaduna ta Arewa, inda ya bayyana goyon bayansa ga Kakakin Majalisar Wakilai, Honarabul Tajuddeen Abbas.

A cikin wata sanarwa da iyalansa suka fitar a ranar Talata, 21 ga Afrilu 2026, mai dauke da sa hannun Alhaji Ahmad Bamalli, an ce an dauki wannan mataki ne bayan shawarwari da aka gudanar tare da la’akari da wasu dalilai na musamman.

Advertisement

Sanarwar ta bayyana cewa Sha’aban ya janye takarar ne bisa muradun iyalansa, tare da jaddada cewa ba zai sake neman wata kujera ta siyasa a Jihar Kaduna a halin yanzu ba.

Sai dai ya tabbatar da cewa zai ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar APC, yana mai cewa a shirye yake ya bayar da gudunmawarsa domin samun nasarar jam’iyyar a jihar da ma kasa baki daya.

Advertisement

Haka kuma, sanarwar ta ce Sha’aban zai mara wa dukkan ‘yan takarar da APC ta tsayar baya, tare da kira ga magoya bayansa da al’ummar Kaduna ta Arewa da su fahimci wannan mataki.

A karshe, iyalansa sun gode wa al’ummar jihar bisa goyon baya da addu’o’in da suke ci gaba da yi masa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending