Connect with us

News

Allah Ya Yiwa Tsohon Shugaban Hukumar KNUPDA Rasuwa Wato TPL Alhaji Isyaku Mukhtar Kura

Published

on

IMG 20260429 011640 325

Allah Ya yi wa tsohon Shugaban Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano (KNUPDA), TPL Alhaji Isyaku Mukhtar Kura rasuwa a daren ranar Talata, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar wa Arewa Radio 93.1.

Marigayin, wanda ya rasu yana da shekaru 74, ya kasance ɗaya daga cikin fitattun masu ruwa da tsaki a harkokin raya birane a Kano, inda ya taba rike mukamai daban-daban a gwamnatocin jihar.

Advertisement

Iran Ta Kunyata Amurka A Idon Duniya A Wannan Yakin Da Suke Yi —Shugaban Gwamnatin Jamus

A baya, ya yi aiki a matsayin Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka a lokacin gwamnatin tsohon gwamna, Sanata Sabo Bakin Zuwo. Haka kuma, ya rike mukamin Manajan Darakta na Hukumar KNUPDA a zamanin gwamnatin Engr. Rabi’u Musa Ƙwanƙwaso.

Advertisement

Wata majiya daga cikin iyalansa ta ce marigayin ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama.

A cewar Faruk Sabo Bakin Zuwo, za a gudanar da sallar jana’izar marigayin a ranar Laraba da karfe 10:00 na safe a gidansa da ke unguwar Hotoro, a tsallaken NNPC Depot kusa da ofishin AA RANO.

Advertisement

 

Allah Ya jikansa da rahama.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending