News
Wata Tirela Ta Murkushe Adaidaita Sahu
Aƙalla mutane biyu sun rasa rayukansu, yayin da wasu biyar suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a yankin Obere da ke kan hanyar Ota–Idiroko a Jihar Ogun da ke kudancin Najeriya.
Rahotanni na nune da cewa hatsarin ya faru ne da sanyin safiyar Talata, bayan wata babbar mota ta kwace ta kutsa cikin wasu ababen hawa a kan babbar hanyar.
Cutar Sankarau Ta Hallaka Mutane Da Dama A Sakkwato
Mai magana da yawun Hukumar Kula da Bin Dokokin Tuki ta Jihar Ogun (TRACE), Babatunde Akinbiyi, ya shaida cewa mutane 21 ne hatsarin ya rutsa da su, ciki har da maza tara da mata goma sha biyu.
Ya kara da cewa daga cikin wadanda abin ya shafa, mutane biyar—maza biyu da mata uku—sun jikkata, yayin da maza biyu suka mutu nan take.
A cewar shaidu, direban babbar motar ya rasa ikon sarrafa ta ne sakamakon barci da kuma gudun wuce gona da iri.
Jami’an TRACE tare da hadin gwiwar Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) sun kai dauki a wurin domin taimakawa wadanda suka jikkata
An garzaya da wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti, yayin da aka ajiye gawarwakin mamatan a Babban Asibitin Ilaro.
