News
Cutar Sankarau Ta Hallaka Mutane Da Dama A Sakkwato
Mazauna ƙauyen Kurawa da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a jihar Sakkwato sun shiga halin fargaba sakamakon ɓarkewar cutar Sankarau, wadda ta yi sanadiyyar asarar rayuka da dama a cikin al’umma.
Rahotanni daga asibitin yankin sun nuna cewa annobar na ƙara tsananta a ‘yan kwanakin nan, inda ake samun mutuwar mutane biyu zuwa uku a kowace rana. Galibin waɗanda cutar ke kashewa sun haɗa da yara da matasa, musamman masu ƙasa da shekaru 20.
Iran Ta Kunyata Amurka A Idon Duniya A Wannan Yakin Da Suke Yi —Shugaban Gwamnatin Jamus
Majiyoyi daga cikin al’ummar yankin sun bayyana cewa ana samun tururuwa na marasa lafiya zuwa cibiyoyin kiwon lafiya domin neman agaji, yayin da ake ci gaba da fargabar yaduwarta cikin sauri a tsakanin jama’a.
An kuma ruwaito cewa wasu daga cikin waɗanda cutar ta kama na rasa rayukansu cikin sa’o’i 24 bayan fara bayyana alamomi, yayin da wasu ke mutuwa a gidajensu kafin su samu damar kai wa asibiti.
Alamomin da aka fi gani sun haɗa da zazzaɓi mai tsanani, ciwon wuya, amai, gudawa da kuma suma — lamarin da ke nuna hatsarin da cutar ke tattare da shi idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba.
Da yake magana kan lamarin, basaraken ƙauyen Kurawa, Malam Mudassir Abdullahi Kurawa, ya bayyana cewa akalla mutane tsakanin 10 zuwa 15 ne suka rasu a ƙauyen kaɗai tun bayan ɓarkewar cutar kimanin makonni uku da suka gabata.
Mazauna yankin na kira ga hukumomin lafiya da su gaggauta kai ɗauki, musamman ta hanyar samar da magunguna, rigakafi da kuma wayar da kan jama’a domin dakile yaɗuwar wannan annoba mai haɗari.
