Connect with us

News

An Ci Tarar Ɗan Najeriya Da Matarsa Dala Miliyan 1 Kan Sare Bishiyoyi Ba Bisa Ka’ida Ba A Amurka

Published

on

bernard and wamer (1)

Majalisar birnin Oakland da ke ƙasar Amurka ta umarci wani likita ɗan Najeriya, Matthew Bernard, da abokiyar zamansa Lynn Warner su biya kusan dala miliyan 1 a matsayin tara, sakamakon sare bishiyoyi a kusa da gidansu da ke kan titin Claremont Avenue.

An ɗauki wannan mataki ne bayan shafe shekaru ana takaddama tsakanin masu gidan da hukumomin birnin kan sare bishiyoyi ba tare da izini ba.

Advertisement

Kuskuren Harin Dakarun Sojin Sama Ya Sake Hallaka Tarin Fararen Hula A Neja

A yayin zaman sauraron, Bernard ya kare kansa inda ya shaida wa mambobin majalisar cewa bishiyoyin da aka sare kusan shekaru huɗu da suka wuce “sun mutu ne, suna mutuwa, sun karkata,” ko kuma suna cikin “haɗarin faɗuwa.”

Advertisement

Likitan ɗan Najeriyan ya kuma nemi izinin sake dasa bishiyoyi bayan an kammala gine-ginen da ake shirin yi a wurin, amma an ƙi amincewa da buƙatar.

A maimakon haka, hukumomin birnin sun ci tarar dala 915,135.40 ga Bernard da Warner, tare da ɗora takunkumi (lien) kan kadarar, wanda ke hana sayarwa ko bunƙasa filin har sai an biya tarar gaba ɗaya.

Advertisement

 

PM NEWS

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending