Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mutane Hudu Dauke Da Kokon Kan Mutun A Kwara

Published

on

images (3)

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara ta kama wasu mutane huɗu bisa zargin hannu a cire kawunan gawarwaki daga kaburbura da kuma mallakar hannayen mutum da ake zargin an tanada domin tsafin neman kuɗi.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Ojo Adekimi, ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Ilorin.

An Sare Wa Matashi Hannu Kan Rikicin Siyasa A Bauchi

Ya ce a lamarin farko, an kama Abu Jimoh da Ayo Jimoh bisa zargin haƙo kaburbura da cire kawunan gawarwaki a wata makabarta da ke Omupo.

 

A cewarsa, an gano lamarin ne a watan Mayun 2026, lokacin da wasu mazauna yankin suka je makabartar domin binne mamaci, inda suka gano an haƙo wasu kaburbura kuma kawunan gawarwakin da ke cikinsu sun ɓace.

Advertisement

Kwamishinan ya ce jami’an ’yan sanda sun kama waɗanda ake zargin da misalin ƙarfe 5:00 na safiyar 8 ga Oktoba, 2026, yayin da ake zargin suna haƙa kaburbura a makabartar.

Ya ƙara da cewa, yayin bincike, waɗanda ake zargin sun ambaci wani mai maganin gargajiya mai suna Mukaila Bello, wanda suka zarga da sayen kawunan gawarwakin.

Sai dai, rundunar ba ta bayyana ko an kama Bello ba, yayin da ta ce ana ci gaba da bincike kan lamarin.

A wani lamari na daban, ’yan sandan sun kama Kamalden Lukmon da AbdulGaniyu Ibrahim bayan gano wasu hannayen mutum guda biyu da ake zargin sun mallaka a kan titin Bakase da ke Alapa.

A cewar rundunar, an kama mutanen ne da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin ranar 8 ga Oktoba, inda binciken farko ya nuna cewa ana zargin sun yi niyyar amfani da sassan jikin wajen tsafin neman kuɗi.

Rundunar ta ce waɗanda ake zargin sun bayyana cewa wani jami’in tsaro na sa-kai mai suna Abdulraf Apata ne ya miƙa musu hannayen.

Advertisement

Kwamishinan ya ce ana binciken zargin da ake yi wa Apata domin gano gaskiyar lamarin da kuma tantance ko akwai wasu mutane da ke da hannu a ciki.

Ya ƙara da cewa ana tsare da Lukmon da Ibrahim a sashen rundunar da ke yaƙi da manyan laifuka, yayin da ake ƙoƙarin gano wanda sassan jikin suka fito daga gare shi da kuma yanayin mutuwar da ke da alaƙa da binciken.

Rundunar ta ce za ta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

 

 

PUNCH

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending