Labarai
Majalisun Dokokin Jihohi 36 Sun Amince Da Ƙudirin Kafa Ƴansandan Jihohi

Dukkan majalisun dokokin jihohin Najeriya 36 sun amince da ƙudirin gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar da ke neman bai wa jihohi damar kafa rundunonin ’yan sandan kansu.
Magatakardan Majalisar Dokokin Tarayya, Kamoru Ogunlana, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 16 ga Nuwamba, 2026.
Shugaban Kasar Mongolia Ya Yi Murabus Sakamakon Zargin Cin Hanci Da Rashawa
Ya ce amincewar da dukkan majalisun dokokin jihohin suka bayar ta kai kashi 100 cikin 100, wanda hakan ya zarce mafi ƙarancin kashi 75 cikin 100, wato majalisu 24, da sashe na 9(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada domin yin gyara.
Ogunlana ya bayyana cewa Majalisar Dokokin Tarayya ta kammala tantance takardun amincewar da jihohin suka aika, inda ta tabbatar da cewa ƙudirin ya cika dukkan sharuɗɗan da ake buƙata domin miƙa shi ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, don amincewa.
A cewarsa, an jinkirta miƙa ƙudirin ne domin bai wa dukkan jihohin damar kammala tattaunawa da kuma bayyana matsayarsu kan batun.
Ƙudirin, wanda ya ƙunshi gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999, zai samar da tsarin doka da zai bai wa jihohi ikon kafa rundunonin ’yan sandan kansu, baya ga rundunar ’yan sandan tarayya.
Idan Shugaban Ƙasa ya amince da ƙudirin tare da sanya hannu a kansa, jihohi za su samu damar kafa rundunonin ’yan sandan da za su kula da tsaro a yankunansu, tare da taimakawa wajen dakile laifuffuka da ƙarfafa ayyukan tsaro.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan buƙatar sauya tsarin tsaron Najeriya, musamman ta fuskar bai wa jihohi ƙarin iko da damar tunkarar matsalolin tsaro da suka addabi sassa daban-daban na ƙasar.
Sai dai, duk da amincewar da majalisun dokokin jihohin suka bayar, ƙudirin na buƙatar amincewar Shugaban Ƙasa kafin ya kammala matakin zama doka.
-
Labarai7 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai3 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai2 days ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
