Connect with us

Labarai

Majalisar dattawa ta miƙa wa Tinubu ƙudirin samar da ƴansandan jihohi

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Majalisar dattawar Najeriya ta umarci akawunta ya tura wa shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu, ƙudirin dokar samar da ƴansandan jihohi da suka amince ta ita, don sanya hannu ta zama doka.

Wannan dai ya biyo bayan mahawarar da ƴan majalisar suka tabka, sakamakon amincewa da ƙudirin da majalisun dokokin jihohin ƙasar 36 suka yi, lamarin da ake kallo a matsayin yunƙurin kawo ƙarshen matsalar tsaro da garkuwa da mutane da ta’addanci da ke damun ƙasar.

PAN Ta Bukaci Gwamnatoci Su Bai Wa Noma Da Kiwo Muhimmanci Kamar Tsaro

A lokacin da shugaban masu rinjaye na majalisar Sanata Opeyemi Bamidele ke jagorantar mahawarar, ya ce a watannin Yuni da kuma Yuli ne ƴan majalisar suka amince da ƙudirin, wanda ya samu amincewar kashi biyu bisa ukunsu kamar yadda doka ta tanada.

Haka nan ya ce suma dukkanin majalisun johohi 36 na Najeriya sun amince da ƙudirin dokar, lamarin da yayi dai-dai da tanadin sashi na 9 na kundin dokar Najeriya na shekarar 1999.

Ƴan majalisar sun kuma yaba wa shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa goyon bayan da ya nuna wajen samar da dokar kafa ƴansanda jihohi.

RFI

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending