Connect with us

News

Shafin Youtube ya amsa kiran Saudiyya, ya cire tallace-tallacen da suka saɓa wa Musulunci

Published

on

Advertisements
ads

DAGA MARYAM BASHIR MUSA

 

 

 

Shafin YouTube ya cire tallace-tallacen da hukumar kula da harkokin yada labarai ta Saudiyya ta yi Allah wadai da su da cewa sun saba wa kimar Musulunci ta kasar.

 

Advertisement

A wata sanarwa da shafin ya wallafa a shafinsa na Twitter, YouTube ya ce ba za a amince da tallace-tallacen ba, kuma ya dauki matakin gaggawa don dakatar da abin da ya kira masu cin zarafi da ke karya manufofin kamfanin.

CBN ta baiwa TajBank lasisin gudanar da harkoki a faɗin ƙasa

Matakin na zuwa ne kwanaki kadan bayan da kafafen yada labarai da hukumomin fasaha a Saudiyya suka yi gargadin cewa za a dauki matakan shari’a idan har YouTube bai dakatar da tallace-tallacen da ake gani a kasar ba.

 

Hakan ya biyo bayan wani kamfe da wasu ‘yan kasar Saudiyya suka yi ta Internet, inda suka koka kan yadda yara ke tallan da ba su dace ba a YouTube.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending