News
Buhari zai ƙaddamar da Dalar shinkafa a Abuja
Daga kabiru basiru fulatan
A ranar Talata Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da gagarumar Dalar shinkafa ta Babban Bankin Nijeriya, CBN a Abuja.
Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito cewa CBN ne da Ƙungiyar Manoma Shinkafa, RIFAN su ka haɗa gwiwa wajen samar da ita.
Bayanan da a ka samu da shafin yanar gizo na CBN din sun nuna cewa an samar da Dalar, wacce a ka ce ita ce mafi girma a duniya, ta Shirin Baiwa Manoma Tallafi, wanda a ka fi sani da Anchor Borrowers Programme, ABP.
Bayanan sun baiyana cewa shirin tallafin manoman, wanda a ka samar da shi a 2015, ya ƙara noman shinkafa da ga tan miliyan 1.8 zuwa biyar , inda kuma ya daƙile shigo da shinkafar cikin gida Nijeriya.
Haka zalika shirin ya sanya taguwar kashe kuɗaɗe wajen shigo da shinkafa da ga dala biliyan 1.5 zuwa dala miliyan 18.5 a shekara.
Ya kuma samar da aikin yi na kai tsaye da wanda ba na kai tsaye ba har miliyan 12.8 a bangaren hatsi da dama.
NAN ta rawaito cewa an samar da Dalar shinkafar ne a filin bajakoli na Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu da ke Abuja.
-
News5 days ago
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
-
News6 days ago
An Tura Kwamishinonin ’Yansanda 30 Da Jami’ai 15,000 Domin Sanya Ido A Zaɓen Osun
-
News3 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
