Connect with us

News

Ganduje Ya Sha Alwashi Sai An Hukunta Dan Chinan Da Ya Yi Ajalin Budurwarsa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce lallai za’a dauki matakin Shari’a akan dan kasar China da ya kashe tsohuwar budurwar sa mai suna Ummulkairi Sani a unguwar Dorayi Babba a karamar hukumar Gwale.

Ganduje ya Bayyana Hakanne a wajen Bikin Kaddamar da Sabbin Kwamitocin Hukumar Shari’a ta Jihar kano da Hukumar zakka da Hukumar Hisbah wanda aka yi a dakin taro na Coronation Hall dake fadar gwamnatin kano.

Advertisement

Wadanne Shugabannin Duniya Aka Gayyata Bikin Binne Sarauniya Elizabeth II?

Gwamna Ganduje ya ce “Mun sami labarin dan kasar China da ya kashe wata budurwar sa, lamarin bai mana dadi ba sam kuma akwai abun bakin ciki”

Advertisement

“Kuma lallai baza’a bar shi haka ba, mun sa an kama shi domin hukunta shi akan abun da ya aikata”.

Ma’aikatar Shari’a akwai babban aiki a gaban ku game da wannan lamarin” a cewar gwamna Ganduje.

Advertisement

Gwamnan ya kuma addu’ar Allah ya ji kan ta da gafara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending