News
Wadanne Shugabannin Duniya Aka Gayyata Bikin Binne Sarauniya Elizabeth II?
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Daruruwan shugabanni da masu rike da sarautun gargajiya daga sassa daban-daban na duniya ne ake sa ran za su halarci bikin binne sarauniya Elizabeth II da zai gudana ranar Litinin a birnin Landan na Birtaniya.
Bikin dai an yi ittfikafin shi ne irinsa da zai fi hada shugabannin duniya a tsawon shekaru masu yawa.
Soludo ya hana sanya ɗangalallen siket a matsayin tufafin makaranta a Anambra
Za dai a binne ta ne a Westminster Abbey da ke Landan, wanda yake da fadin cin kusan mutum 2,000, kuma shugabannin kasashe kusan da wakilansu kimanin 500 ne ake sa ran za su halarta, kafar yada labarai ta BBC ta rawaito.
Kazalika, iyalan marigayiya Sarauniyar da kawayenta da abokan arziki da sauran manyan mutane da ’yan siyasar Birtaniya ma za su halarta.
Aminiya ta zakulo muku jerin fitattun shugabannin da aka gayyata wajen bikin daga Shugabannin Kasashe ko Firaministoci da sarakunan gargajiya da kuma ma wadanda ba a gayyata ba.
Ga wasu daga cikinsu:
Sarakunan gargajiyar da aka gayyata
Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman,
Galibin sarakunan gargajiyar da ke Tarayyar Turai za su halarta
Basaraken Japan, Naruhito da mai dakinsa, Empress Masako
Sarkin Holland, Willem-Alexander
Sarauniya Maxima da Gimbiya Beatrix
Sarki Philippe na Belgium
Sarki Harald V na Norway
Yarima Albert II na Monaco
Sarauniyar Denmark, Margrethe
Sarkin Spain, Felipe VI da mai dakinsa, Letizia
Shugabannin Kasashen duniya
Shugaban Amurka, Joe Biden da matarsa,
Matar Shugaban Ukraine, Olena, Volodymyr Zelensky
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Brazil, Jair Bolsonaro
Mataimakin Shugaban Kasar China, Wang Qisha
Shugabar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen
Shugaban Majalisar Tarayyar Turai, Charles Michel
Shugaban Italiya, Sergio Mattarella of Italy
Ministan Harkokin Wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier
Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Isaac Herzog
Ministan Harkokin Wajen Koriya ta Kudu, Yoon Suk-yeol
Firaministan Arewacin Ireland, Micheal Martin
Firaministan Kanda, Justin Trudeau,
Firaministan Australiya, Anthony Albanese
Firaministan New Zealand, Jacinda Ardern
Mataimakin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo
Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa
Firaministan Bangladesh, Sheikh Hasina,
Shugaban Sri Lankan, Ranil Wickremesinghe
Firaministan Fiji, Frank Bainimarama
Wadanda ba a gayyata ba
Shugaban Rasha, Vladimir Putin
Shugaban Iran,
Shugaban Nicaragua
Shugaban Koriya ta Arewa
Shugaban Belarus
Gwamnatin Taliban ta Afghanistan
Shugabannin kasashen Myanmar da Siriya da Venezuela
(AFP)
