Connect with us

News

Soludo ya hana sanya ɗangalallen siket a matsayin tufafin makaranta a Anambra

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

 

 

 

Advertisement

 

 

Gwamnatin Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ta hana sanya ɗangalallen siket a matsayin tufafin zuwa makaranta a dukkan makarantun jihar.

 

Kwamishiniyar ilimi ta jihar, Ngozi Chuma Udeh ce ta bayyana hakan a garin Awka a yau Lahadin da ta gabata, inda ta ce sanarwar dakatarwar ta zama wajibi ganin yadda makarantu za su koma hutu a gobe Litinin.

Wasiyyar Marigayi Sheikh Ja’afar Ga Matasa Lokacin Siyasa‘m

Advertisement

Ta ce an sanar da dakatarwar ga sakatarorin ilimi na makarantun gwamnati, har ma da masu zaman kansu a jihar.

 

Kwamishiyar ta yi Alla-wadai da yadda ake samun ƙaruwar sanya kananan kaya a matsayin kayan makaranta, sannan ta ce yin hakan rashin tarbiyya ne da gwamnati ba za ta lamunci hakan ga ɗaliban makaranta ba.

 

“Ya kamata ɗalibi ya yi shiga ta mutunci ya nuna kyakkyawan yanayi kuma kada ya kasance cikin suturar da ba ta dace ba don makaranta.

 

Advertisement

“Tsarin da aka yarda da shi shine riguna a na tufafin makaranta cikin jihar su kasance tsayin gwiwa kuma baya sama da gwiwa, wanda ke saurin zama yanayin salo a makarantu,” in ji ta.

 

Kwamishiniyar ta ce an tuhumi Sakatarorin Ilimi don tabbatar da cewa makarantu sun bi umarnin don ceto makomar daliban jihar.

 

 

 

Advertisement

DAILY NIGERIAN

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending