Connect with us

News

An Cafke Matashi Kan Sukar Gwamnan Yobe A Kafafen Sada Zumunta

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Wani matashi mai shekara 16 ya shiga hannun hukuma bayan an zarge shi da cin zarafin Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni a kafafen sada zumunta.

 

Advertisement

Jami’an tsaro sun cafke matashin tun a ranar 11 ga watan Disamba, 2022 amma labarin bai bayyana ba sai a ranar Litinin lokacin da mahaifin yaron ya bukaci a sakar masa da.

 

Advertisement

Yadda ƴan sanda suka nemi hallaka ma’aikacin Premier Radio.

Rahotanni sun ce an cafke matashin ne a garin Nguru, wanda daga bisani kuma aka dauke shi zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar ’Yan Sanda Jihar da ke Damaturu.

 

Advertisement

Aminiya ta rawaito cewa Mahaifin yaron mai suna Garba Haruna, wanda ke sana’ar wanki da guga, ya roki Gwamnan Jihar da Kwamishinan ’Yan Sandan jihar da su saki dansa.

 

Advertisement

 

“Na yi nadamar abin da dana (Umar) ya aikata. Ni ba kowa ba ne face mai wanki da guga, ina rokon Gwamna Mai Mala Buni da ’yan sanda da su taimaka su yafe masa kuma su sake shi,” inji mahaifin yaron.

Advertisement

 

Da aka tuntubi Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, ya ce yaron yana tsare kuma da zarar sun kammala bincike za su mika shi zuwa kotu.

Advertisement

 

“Da zarar mun kammala bincike za a mika shi kotu. Mutane suna amfani da kafafen sada zumunta wajen bata sunan mutane, don haka akwai bukatar kawo gyara a cikin al’umma.

Advertisement

 

“Ba zai yiwu mutane su rika wallafa duk abin da suka ga dama ba. Akwai doka da oda a Najeriya. Duk wanda aka samu da laifi dole ne ya fuskanci hukunci,” cewar Kwamishinan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending