Connect with us

News

An Kama Dalibai 2 Da Wasu Iyaye Kan Zargin Kirkirar Makin Jarrabawar JAMB

Published

on

jamb exam1 (1)

Hukumar kula da zana jarrabawar shiga jami’a ta Nijeriya, JAMB ta sanar a ranar Jumma’a cewa an kama wasu ɗalibai biyu da wasu iyaye kan zargin amfani da fasahar Ƙirƙirarriyar Basira, AI wajen karkatar da sakamakon jarabawar UTME ta ta 2026.

Mai magana da yawun JAMB, Fabian Benjamin, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa an kama mutanen ne saboda sauya sakonnin sakamakon jarabawa da ake turawa ta SMS, domin kirkira ko canza makin dalibai da nufin yaudarar wasu, ciki har da iyaye.

Dakarun Soji Sun Kama Mutum Da Manyan Makamai Da Kayayyakin Ƙera Bama-bamai A Hanyar Kaduna ‎

Sanarwar ta ce: “A halin yanzu, ɗalibai biyu da wasu iyaye suna tsare saboda hannu a karkatar da sakamako ta amfani da AI da sauran hanyoyin intanet.”

Wannan sanarwa ta zo ne a daidai lokacin da hukumar ta fitar da sakamakon ɗalibai 632,788 da suka rubuta jarrabawar a ranar Alhamis, 16 ga Afrilu.

Benjamin ya gargadi cewa irin wannan aiki babban laifi ne, yana mai cewa hukumar za ta hukunta duk wanda aka samu da laifi gwargwadon dokar kasa.

Advertisement

An fara rubuta jarabawar UTME ta 2026 ne a ranar 16 ga Afrilu kuma ana sa ran za a ci gaba har zuwa ranar 22 ga Afrilu a cibiyoyin jarrabawa a fadin kasar. Ana ci gaba da fitar da sakamakon ne a rukuni-rukuni yayin da ake gudanar da jarabawar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending