News
Motar Tifa Ta Murƙushe Mutum 3 Har lahira
Mutane uku, ciki har da wani karamin yaro, sun mutu a wani hatsarin motar Tifa da ya afku a titin Abeokuta–Sagamu a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a yankin Daywaterman, kusa da Onipepeye, kamar yadda Hukumar Kula da Harkokin Tuki da Bin Dokokin Hanya ta jihar Ogun (TRACE) ta tabbatar.
Kujerar Mataimakin Gwamna : Jaddada Matsayata Da Kalubalantar MUNAFUKAI
Mai magana da yawun hukumar, Babatunde Akinbiyi, ya ce hatsarin ya shafi wata babbar Motar Tifa da kuma karamar mota kirar bas.
A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa direban Tifa ya yi tukin ganganci, inda ya bugi karamar motar.
Ya kara da cewa motocin da abin ya shafa ba su da lambobin rajista, inda babbar motar kirar Dongfeng ke dauke da alamar ma’aikatar muhalli, yayin da karamar motar kuma aka kawata ta da tambarin yakin neman zabe.
Mutane biyar ne hatsarin ya rutsa da su, inda mata biyu suka jikkata, yayin da mutum uku da karamin yaro da maza biyu suka rasa rayukansu nan take.
An kai gawarwakin wadanda suka mutu zuwa asibitin gwamnati na Ijaye, yayin da aka ce ‘yan uwan wadanda suka jikkata ne suka garzaya da su asibiti kafin isowar jami’an ceto.
Hukumar FRSC da jami’an agajin gaggawa sun isa wurin domin daukar matakan da suka dace.
PUNCH
