News
Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Sanata, Ibrahim Shekarau, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP a hukumance.
A wata wasiƙar murabus da ya aike a yau Lahadi, 19 ga Afrilu, 2026, zuwa ga shugabannin jam’iyyar a unguwar Giginyu da ke ƙaramar hukumar Nassarawa, Shekarau ya bayyana cewa ya yanke wannan shawara ne bayan tattaunawa mai zurfi da mambobin ƙungiyarsa ta siyasa.
Motar Tifa Ta Murƙushe Mutum 3 Har lahira
Tsohon gwamnan ya ce ya shirya komawa wata jam’iyya domin ci gaba da harkokinsa na siyasa, duk da cewa bai bayyana sunan sabuwar jam’iyyar ba a cikin wasiƙar.
Sai dai ya yaba da shugabannin jam’iyyar ta PDP, inda ya bayyana su a matsayin nagartattu, tsu.
An kuma aika kwafin wasiƙar ga shugaban PDP na jihar Kano da kuma na ƙaramar hukumar Nassarawa, a matsayin sanarwa a hukumance kan matakin da ya ɗauka.
