News
Ya kamata Gwamnatin Tarayya Ta Gaggauta Janye Karin Kudin Wutar Lantarki – SERAP
DAGA HASSAN KHALID HAMZA
Kungiyar kare ‘yancin harkokin zamantakewa da na tattalin arziki ta SERAP, ta buƙaci Shugaba Muhammadu Buhari da ya yi gaggawar janye ƙarin kuɗin wutar lantarki da aka yi ba bisa ka’ida ba a watan Disamban 2022.
Kungiyar ta bukaci shugaban kasa da ya umarci ministan wutar lantarki, Goddy Jedy-Agba da shugaban hukumar kula da hasken wutar lantarki ta Najeriya (NERC), Farfesa James Momoh da su gaggauta janye karin kudin wutar lantarkin.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya bukaci Buhari ya “tabbatar da binciken kashe kuɗaɗen jama’a a matsayin ‘zuba jari da ceto’ da gwamnatocin baya suka yi wa kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) da kamfanonin samar da wutar lantarki (GenCos) tun 2005 da kuma gurfanar da wadanda suke da hannu gaban kuliya.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa biyo bayan amincewar da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya ta bayar, an kara kudin wutar lantarki a fadin kamfanin rarraba wutar lantarki na kasar nan a watan Disambar 2022. Wasu kwastomomin da dama sun tabbatar da karin kudin.
Ministan wutar lantarki da NERC duk sun ki tabbatarwa ko musanta ƙarin kudin.
